YUNWA: Gwamnatin Najeriya na Bukatar ta maida hankali sosai wajen wadata kasa da abinci

1

Darektan wata kungiya mai zaman kanta wato Civil Society Organisation CS-SUN kuma memban kungiyar PACFaH, Beatrice Eluaka ta koka da rashin maida hankali da kasa Najeriya ba ta yi wajen kawar da yunwa da ake fama dashi a sassan kasar abin tashin hankali ne.

Ta fadi hakan ne a taron da masana su kayi a garin Kaduna kan matsalar yunwa inda suka tattauna akan yadda za a nemo matakan da gidajen jarida za su yi amfani da su domin ganin cewa an shawo kan yuwan da kasan ke fama da shi.

Eluaka ta ce kamar yadda rahotan hukumar NDHS ta shekaran 2013 ya nuna cewa yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamacin kasa Najeriya sune suka fi fama da matsalar yunwa musamman kananan yara ‘yan kasa da shekara biyar.

Ta ce bisa ga rohotan kashi 27.1 da kashi 19.5 bisa 100 sune yawan adadin yaran dake fama da yunwa sannan kashi 30.8 da kashi 47.4 bisa 100 sune yawan adadin yaran da yunwa ta hana su girma yadda ya kamata a yankuman arewa maso yamma da arewa maso gabacin kasa Najeriya.

Jane Gwani wakiliyar jihar Kaduna ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta hada hannu da asusun bada talafi ga kananan yara UNICEF domin ganin cewa sun samar kudaden da za a bukata domin kawar da yunwa a jihar.

Wakiliyar jihar Nasarawa Amina Isah ta ce jihar Nasarawa ta kafa kwamitin samar da abincin da mutane ke bukata sannan kuma ta bude wata asusu domin samar da kudaden da zai taimaka wajen wadata mutanen jihar da abinci.

Share.

game da Author