‘Yan daba sun sari Ahlan Sheriff da adda

0

Wasu matasa da ake kyautata zaton ‘yan daba ne, sun Sassari fitaccen dan was Ahlan da adda a gefen goshin sa, da gadon bayan sa. Sanadiyya wannan sara da aka yi masa, Ahlan ya samu mummunan rauni, wanda tuni aka sallame shi daga asibiti.

Wannan hari da aka kai masa, ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda Nasir Gwangwazo, fitaccen masubucin labaran finafinan Hausa ya bayyana wa Premium Times Hausa. Kokarin samun Ahlan a waya bai yiwu ba, domin ta na kasha. Sai dai kuma Gwamgwazo ya ce a zaman yanzu Ahlan ya na gida, kuma ya na samun sauki.

shahararren dan fim kuma furodusa ne, wanda ya yi fice wajen iya fitowa a matsayin mai zabga Turanci gangariya a finafinan Hausa. Kuma a zaman yanzu an rage ganin sa cikin ‘yan fim, saboda ya fi maida hankali ga aikin sa na koyarwa da ya ke yi a Kwalejin Ilmi Mai Zurfi ta Sa’adatu Rimi, da ke Na’ibawa, Kano.

Kadan daga cikin finafinan da ya yi, sun hada da: Jinsee, 419, Mafiya da Gadon Baya da sauran su.

An kai masa harin ne a unguwar Kabuga Janbulo in da yake Zaune.

Share.

game da Author