Yau ne za a yi karawar karshe a wasan kwallon kafa na kasar Spain inda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ke neman ta buga kunnen doki kawai a wasanta da Malaga, ita kuma Barcelona ta na neman dole ta ci wasa ne kuma dole sai Madrid ta sha kashi koda ta ci za ta iya zama zakara.
Yanzu dai abin da kamar wuya ga Barcelona sai dai kuma babu ta inda kwallon kafa bata kayawa.
Idan dai Malaga ta doke Madrid zata samu kyautar kudi £600,000 amma idan Madrid ta doke ta zata samu kyautar Miliyan £1.