Wasu mazaunan kauyen Etogi na mazabar Gbara dake karamar hukumar Mokwa a jihar Neja sun ki komawa matsugunin su dalilin harin da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai kauyensu inda yayi sanadiyyar rayuka da dama.
Wadanda suka kai wannan harin sun bude wuta a wani masallaci daidai masallata na sallar Asuba in da suka kashe mutane 20 nan take.
Shima limamin da yake jan sallar a wannan lokaci bai tsira da ran saba.
Ana zargin cewa fulani makiyaya ne suka kai wannan hari.
Wasu daga cikin mutanen kauyen da suka gudu lokacin da abin yake faruwa zuwa kauyen Kpata Katcha sun ce Allah ne ya sa da sauran kwanansu a gaba.
Wani jami’in dan sandan wanda ya nemi a boye sunansa ya fada wa gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa bayan sun kashen mutanen da ke masallacin sai suka shiga cikin kauyen inda suka sace dukiyoyin wasu attajirai mata sannan suka kashe su.
“ Bayan haka da suka gama abinda za suyi a gidajen mutanen sai suka koma shagunan da mazauna kauyen ke caja wayoyinsu suka kwashe su tas.”
Dan sandan ya ce mai yiwuwa ne harin da aka kawo wannan kauyen ramuwar gaiya ce na kisan dan uwansu da mazaunan kauyen suka yi a kwanakin baya.
” A kwanakin da suka wuce mazaunan kauyen sun kafa dokar da ya hana makiyayan wucewa ta garinsu wanda garin hakan ne ya kawo rikici tsakin su.’’
Wasu mazaunan kauyen sunce mutanen sunyi musu barazanar dawowa kauyen shine yasa gaba dayansu suka ce ba za su dawo garin ba.
Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar DSP Bala Elkana yace tabas harin da aka kai wannan kauye ya basu mamaki matuka, amma kuma ba zai yiwu ace wai don wannan bafulatani bane da ya rasa ransa a kauyen yasa hakan ya faru.
Yace rundunar ‘yan sandan jihar sun shirya su tun tuni.
Duk da haka Elkana y ace sun tura jami’an tsaron dasuke aikin samar da zaman lafiya a kauyen.
Bayan haka gwamnan jihar Abubakar Bello yace za a hukunta duk wanda aka kama da laifi kan wannan hari.
Ya fadi hakan ne ta bakin kakakinsa Jibirin Ndace a yau Talata inda ya shawarci mutane da su gujewa daukan fansa akan duk abin da ya same su.
Ya kuma shawarci mutanen da su kai karan duk wanda ko kuma abin da suka gani da basu amince da shi ba zuwa ga jami’an tsaro tun da wuri.
Daga karshe mataimakin gwamnan jihar Ahmed Ketso ya jagoranci ma’aikatan gwamanti domin ziyartar kauyen sannan kuma shi gwamnan jihar ya bada gudumawar wasu kudade domin tallafa wa mazaunan kauyen.