Wani lauya ya roki majalisar Dokoki ta tsige Buhari

1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci mataimakinsa Yemi Osinbajo ya ci gaba da gudanar da al’amuran mulki a tsawon kwanankin da zai yi a kasar Britaniya wajen duba lafiyarsa.

Buhari ya sanar da hakanne a wata wasika da ya rubuta wa majalisar dokoki na kasa.

Hakan bai yi ma wadansu dadi ba inda suka nemi majalisar da ta ki amincewa da wannan wasika wai don shugaban kasa ya yi amfani da Kalmar Coordinate wato ya ci gaba da gudanar da ayyukan mulki kamar yadda ya kamata.

Duk da cewa majalisar tayi watsi da wannan tayi da wadansu suka nemi da ayi, mutane a kasa na ta fadin albarkacin bakinsu akan wannan wasika.

Wasu sun ce wai wannan kalma bai ba mataimakin shugaban kasa ikon da zai iya nada ko tsige wani jami’in gwamnati ba. A takaice dai ba kamar yadda ya saba rubutawa ba ne.

Wani Lauya mazaunin jihar Legas Ebun-Olu Adegboruwa ya yi kira ga majalisar dokoki na kasa da ta tsige Buhari a dalilin haka.

Yace bayanan da Buhari ya bada a wasikar da ya mika majalisar bai nuna cewa Osinbajo zai iya yin wani abu ba a kasa Najeriya.

Yayi kira ga ‘yan mjalisa da su fara shirin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Share.

game da Author