Uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ta yi roko a gaban alkalin babban kotun Ikeja da ke Legas cewa, ta taimaka ta kwato mata hakkin ta, a hannun wani fasto wanda da dauki amanar kudi har naira milyan 918 ta damka masa, a matsayin za su yi kasuwanci.
“Da farko na yi tunani kuma na yi amanna cewa a matsayin sa na fasto, ba zai cuce ni ko zambace ni ba. Sannan kuma kasancewa yadda na ga yawan ambaton Allah a baki, ban yi tunani zamba za ta shigo a cikin harkar ba”
Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa Titi Abubakar ce da kanta ta bayyana wa kotun haka a lokacin da ake mata tambayoyi dangane da abin da ta sani a kan tuhumar Fasto Nsikak Abasi Akpan-Jacobs, Abdulmaliki Ibrahim da kuma Dana Motors, Ltd.
Hukumar Hana Ayyukan Cin Hanci Da Zambar Kudade EFCC ce ta gurfanar da su, inda ake zargin su da cin amana, zamba da kuma sata gami da yi wa dukiyar wani hankaka-maida-dan-wani-naka, har na zunzurutun kudi naira milyan 918, mallakar kamfanin THA Shipping Maritime Services Ltd, na matar Atiku.
Da ya ke Hausawa na cewa maso-abinka ya fi ka dabara, lauyan Faston da ake kara, ya yi kokarin yi wa Titi asarkala a gaban alkali, inda a lokacin da ya ke yi mata tambayoyi, ya kalubalance ta dangabe da yadda ta yi amfani da sunaye daban daban a wasu takardun kamfani da harkokin kudi.
“Ran ki ya dade, me ya sa ki ka yi amfani da sunan Florence Doregos a takardar korafin da ki ka kai wa EFCC, wadda kuma da wannan takardar ce aka shigar da kara, a matsayin shaidar farko a kotu? Haka lauya Mista Ibe ya tambayi Titi Abubakar.
Sai dai kuma Titi Abubakar ta maida masa amsar cewa: “Da Florence Doregos da Titi Amina Atiku Abubakar duk sunaye na ne. Lakabin Mrs., wanda ya bayyana a sunan Florence Doregos kuma kuskure ne lauya na ya yi wurin rubutawa.’’
“Florence suna na ne, na rika amfani da sunan Doregos lokacin da muke kan mulki, saboda sunan mahaifina Dorego Albert. Mu ‘yan asalin Ilesha ne, amma ina da dangi har a Jamhuriyar Benin.”
“Don haka zan iya amfani da sunan mahaifi na, ko na miji na. Sunan Dino Melaye na ainihi Daniel Melaye, amma a yanzu Dino ya ke kiran kan sa har a rubuce. Don haka zan iya amfani da duk sunan da na ke so.” Inji Titi.
Da ya ke lauyan faston da ake kara ya murje idanu ya tambayi Titi ya na so ya san asalin ta, nan take ta maida masa amsa da cewa:
“To ni dai na auri miji na cikin 1971, a Ikoyi, kuma yanzu haka akwai sunayen mu a cikin rajistar aure a can. A wancan lokacin ina Kirista na yi aure, da sunan Angelina wanda shi ne sunan yanka na, sunan da iyaye suka rada min kuma Florence.
To bayan mun yi aure sai na shiga addinin Musulunci, aka rika kira na Amina Titilayo.”
Har yau dai Lauya Ibe bai hakura ba, ya sake tambayar ta cewa, amma kuma akwai wani littafi da aka rubuta, na tarihin mijin ta mai suna ‘’Labarin Atiku Abubakar, wanda aka ciki an nuna cewa ita ‘yar asalin jihar Adamawa ce.
Shi ne ita kuma ta maida masa raddi cewa ai tunda dan asalin waccan karamar hukuma ya aure ni, ni ma na zama ‘yar can ke nan, tunda inda mijin ka yake, kai ma can ka ke.
“Kai, ko daga sama ko daga cikin karkashin kasa na fito, duk inda miji na yake, ai ni ma na zma ‘yar can kenan.” Inji Titi.
Lauya Ibe dai ya nemi ya mika kwafen wannan littafi ga kotu a matsayin shaida, amma alkali Oluwatoyin Ipaye, ya ki amincewa, domin maganar yadda aka yi wa naira milyan 918 hadiyar kafuno ake yi, ba katan-katanar sunan Titi ba.
NAN ta ruwaito cewa kamfanin THA Maritime din mallakar ita Titi da Fasto Akpan ne sai kuma wani mai suna Fred Hilmes. An dai kafa kamfanin a cikin 2000.
An tsara cewa Titi ke da kashi 49 na hannun jari, yayin da Akpan da Holmes kowa kashi 25. Daga baya sai Fasto ya zagaye ya sake sabon kasafi, inda ya bai wa kan sa kashi 70, Titi da Holmes kuwa kowa kashi 15. Ya kuma sake wa kamfanin sabuwar rajista, a matsayin kuma shi ne Babban Manajan Darakta.
Daga inda Fasto Akpan ya fara daukar Dala da gammo, shi ne yadda ya saida kamfanin kacokan ga Dana Motors a kan kudi naira milyan 918, kamar yadda EFCC suka gabatar wa kotu rubutattun shaidu tabbatar wannan cinikin biri a sama da aka yi a tsakanin Akpan da Dana Motors.
Wannan kamfani dai ya na a kan Titin Oshodi-Apapa, a rukunin masana’antu na Amuwo-Odofin, mai lamba C63A.
A lolacin da ake bayanai a gaban alkali, lauyan Fasto Akpan ya musanta ikirarin Titi da ta ce ta zuba jari ya kai na naira bilyan 1.2.
“A cikin takardar kofarin da ki ka aika wa EFCC, kin ce in zuba jari na naira milyan 200. A wani bayanin kuma kin ce abin da ki ka zuba, ya kai naira biliyan 1.2. Shin ki na da hujjar cewa kin zuba wannan kudin? “
A haka dai aka yi ta musayar kalamai, har lauyan EFCC ya sa baki inda ya rika kawo hujjojin rashin gaskiyar Akpan. Bayan kuma ita ma Titi ta bayyana yadda kudin da ta zuba su ka kai naira biliyan 1.2
An dai daga karar sai 5 da 6 Ga Yuli, kuma alkali ya ci Akpan tarar Naira dubu 100 saboda jan-kafa.