Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lallasa Las Palmas da ci 4 da 1.
Barcelona ta buga wasan ne a filin Las Palmas.
Shahararren dan wasanta Neymar ne ya saka kwallaye 3 inda Suarez ya ci kwallo na hudun.
Ita kuma Real Madrid ta doke Sevilla da ci 4 da daya. Ronaldo, Nacho da Toni ne suka saka kwallayen a ragar Sevilla.
Har yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na kan gaba a tebur inda yawan kwallaye ya dora ta a saman Madrid. Sai dai kuma kada ka manta Madrid na da kwantan wasa daya.