Tsakanin El-Rufai da Gidan Jaridar Union: El-Rufai ya bayyana a kotu domin kare kansa

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana a wata kotu a Kaduna yau domin fara sauraren karan da ya shigar ya na kalubalantar kagen da gidan jaridar The Union tayi masa kan arziki da kaddarorin da ya mallaka kafin ya zama gwamnan jihar Kaduna.

El-Rufai ya shigar da karar ne watanni kadan bayan an rantsar dashi gwamnan jihar Kaduna.

Gidan jaridar The Union ta rubuto abinda El-Rufai ya mallaka wanda hakan yasa ya maka gidan Jaridar a Kotu cewa tayi masa kage.

Da yake jawabin kare kansa a gaban Alkalin kotun Mairo L. Muhammed, El-Rufai yace shi attajiri ne tun a da domin shi kwararren ma’aikacin kididdiga gine gine ne.

An daga sauraron karar zuwa 15 ga watan Yuli.

Share.

game da Author