TAMBAYA: Mallam inasan nasan hukuncin bude asusun da ake kira da “fixed deposit” a turance?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Fixed Deposit, asusun ajiya (na musamman) ne da za’a ajiye kudi zuwa tsawon wani lokaci a banki, ita kuma banki zata bada bashi da ruwa, shi kuma mai kudin za’a bashi wani kaso na ruwan da kudinsa suka haifar, bayan cikan lokacin da suka iyakance.
A kashin gaskiya, bankuna suna bada rancen (bashi da ruwa) kudade ga ‘yan kasuwa ko kampanoni, kuma suna biyan wannan rance da ruwa ‘Intrest’ kuma shi ne ruwan da ake biyan masu asusun ajiya ta musamman ‘Fixed Deposit. Sabo da haka, malamai sun yi bayani kamar haka:
1. Fixed Deposit, bashi da ruwa ne, kuma HARAMUN ne ga musulmi. Musulmi ba zai yi ta’amuli da irin wadannan bankuna ba sai dai bisa lalura. Kuma idan lalurar ta tilasta shi yin hakan, to, ba zai yi amfani da kudin ruwan ga kansa ba, ko iyalan sa, sai dai ya sadaukar da ita cikin hidima ga al’uma.
2. Kungiyar kasashen musulmai ta duniya O.I.C (Organization of Islamic Conference) da majalisar manyan malaman Jami’ar Azhar sun ba da fatawar haramcin kudin ruwa na Fixed Deposit ko Savings, yayin da suka tabbatar da cewa bashi da ruwa ne wanda Allah da Manzonsa suka haramta da nassin Al-kur’ani da Hadisi. Shahararren malamin addinin musulunci, kuma masani a tsangayan ilimin kudi ‘Accounting’ da ke Jami’ar Ahamadu Bello ta Zaria, Dr. Ahmad Dogarawa, ya ce: haramun ne ta’amuli da kudin ruwa na ‘savings’ ko ‘Fixed Deposit’.
3. Dukk kudin ruwa Interest ana amfani da shi ne domin kyautata rayuwar mabukata da talakawa musulmai. Dukk wanda ya yi haka, hakika ya tsarkake dukiyar sa daga RIBA kuma Allah zai bashi lada akan hakan.
4. Amma duk wanda ya yi amfani da kudin ruwan ga kansa, ko iyalan sa ko wata hidimar kansa, to, lallai ya sabawa Allah, kuma ma ciyin RIBA ne, yayi shirin yin yaki da Allah. Kudin ruwa (RIBA) yana bata dukiya, yana halaka mutum, kuma yana karya tattalin arziki, sannan Allah na saukar da bala’i ga wannan al’uma.
5. Babu shakka ana iya yin ajiya ta musamman ‘Fixed Deposit’ ko ‘savings’ a bankin musulunci kuma asamu riba ta HALAL bisa lura da wadannan abu-buwan da malamai suka tsara don kaucewa RIBA:
a) In dan mai ajiyan ya wakilta bankin da su juya kudin a cikin harkar kasuwanci na halal, kuma dukkan su sun yarda akan ribar da za su bashi. Allah ce a cikin suratun (Nisa’i: aya ta 29): “Ya ku wadanda kuka yi imani! Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da yaudara, face idan yakasance daga kasuwance ne bisa yarjejeniya daga gareku…”
b) Idan a kwai wata Hukuma amintacciya da za ta bada gudunmuwa wajen kayyade ribar da mai ajiyar zai samu, bisa lura da hada-hadar kasuwanci a wannan kasa ko jaha, kuma ribar na iya faduwa ko tashi.
c) Shaykh-ul-Azhar Dr. Muhammad Sayyid Dandawi, a wata fatawa da manyan malaman Jami’ar Azhar suka bada, dogaro da ayar da tagabata (suratun – Nisa’i: aya ta 29) sun halatta irin wanannan mu’alar da kuma duk ribar da aka samu a cikin hakan komai yawanta.
A Nigeria, munada bankuna irin Jaiz, Stanbic IBTC da sauran su, wadan da musulmi zai iya yin ajiyar kudin sa ta ‘Fixed Deposit’ ko ‘savings’a bankin, kuma ribar da ya samu ta HALAL ne komai yawanta. Ya ci, ya sha, ya yi sutura da dukkanin hidimar sa da na iyalansa gaba daya, ba tare da fadawa cikin halaka ba.
Amma idan kasa ta kasance akan tsarin ‘savings’ ko ‘Fixed Deposit’ na RIBA, to, lallai ne malamai su dubi mas’alar ta babin (masalih al-mursalah), don kada a cutar da Musulunci da Musulmai ta hanyan karya tattalin arzikisu.
Allah shi ne mafi sani.
Imam Muhammad Bello Mai-Iyali
Cibiyar yada Addinin Musulunci na
Harakatu Falahil Islam
Barnawa Low – Cost
Kaduna – Nigeria