Sule Lamido zai ci gaba da zama a kurkuku

0

Alkalin dake sauraron karan da aka shigar Kotun majistare dake garin Dutse tsakanin gwamnatin jihar Jigawa da tsohon gwamnan jihar Sule Lamido, Usman Liman ya yanke hukunci da a ci gaba da tsare Sule a gidan Yari har sai kotu ta gama bincike kan bayanan korafe korafen da ke gaban ta.

Ta ce kotu za ta ci gaba da zama ranar hudu ga wata Mayu saboda haka Sule zai ci gaba da zama a kurkuku har sai ranar da ake kyautata zaton za ta bada belin sa.

Magoyabayan Sule sun tada hayaniya a harabar Kotun Inda sai da jami’an ‘yan sanda suka tarwatsa su da barkonun tsohuwa.

Mataimakin sufritandan ‘yan sanda mai kula da bincike ya ce ‘yan sandan sun tasa keyar Sule ne bayan kukan da gwamnatin jihar ta kawo gabanta cewa gwamnan ya umurci magoya bayansa da su ta da hankalin jama’a a zaben kananan hukumomi da za’ a yi a jihar nan bada dadewa ba.

Sule ya ce ” Kafin wannan zabe sai na tabbatar kowani daya daga cikinku ya yi mini rantsuwa da rayuwansa akan wannan abu da muka sa a gaba.

” Ko ma menene ya faru ba zan saurari kukan ku ba. Abin da nake so kawai Inji shine an nemeni da inzo in bada belin kowani dayanku don ko kun fasa ma wani kai ko kuma kun yi ma wani jina-jina domin wannan gwamnatin mahaukata ce.

Share.

game da Author