Sojojin Birtaniya sun kammala horas da jami’an sojojin horaswan Nijeriya 250

0

Wasu zaratan sojojin bada horo na kasar Birtaniya sun kammala bada horo ga sojojin horaswan kasar nan su 250. An dai kammala bayar da horon ne a Makarantar Horas da Kuratan Sojoji ta Depot Nigerian Army, Zaria, inda suka samu horon tunkara da kuma dakile matsalar tsaron da ka iya tasowa a kowane lokaci.

Da ya ke jawabi a wajen bikin kammala horon a Zaria, shugaban tawagar jami’an sojan Birtaniya, Will Hilton, ya bayyana cewa makasudin horaswar shi ne a cusa wa wadanda aka horas din sanin hanyoyi da dabarun yadda za su horas da wasu jami’an sojojin.

Hilton, wanda Kanar din soja ne, ya jinjina wa wadanda suka samu damar karbar horon a karkashin tawagar su, bisa irin juriyar da suka nuna. Ya kuma kara tunatar da su cewa wannan horaswa da aka ba su, matakin farko ne kuma somin-tabin hanyoyin bada horo a matsayin su na jami’an horaswa.

A nasa jawabin, Kwamandan DNA Zaria, Christopher Musa, ya gode wa tawagar sojojin Birtaniya musamman a kan yadda suka nuna kwarewa da bajintar iya aiki a yayin horaswar makonni hudu da suka yi wa jami’an sojojin Nijeriya.

“Tun a tashin farko dai kun fara bada hora ga wasu sabbin kurata 74, kuma nag a irin bambancin da aka samu da kuma kwarewa a wurin wannan horaswa da ku ka ba su.” Ya ci gaba da cewa, “Na ji dadin wannan aiki da ku ka yi, saboda irin nuna shaukin aikin da ku ke yi da kuma yadda ku ke kara wa jami’an mu kwarin guiwa a wurin horaswar.”

Burgediya Janar Musa, ya nanata cewa matasan sojoji da dama suna bakin kokarin su ainun a fagagen fama. “Su kan su matasan sojojin nan sun ce min na mika godiyar su gare ka, saboda ka cusa musu karin karsashi da hobbasa a rayuwar su ta aikin soja.”

Tun da farko sai da babban mai bayar da horo ga ga kuratan sojoji na makarantar, Kanar Auwalu Haruna, shirin horas da masu horaswa din nan wani kwas ne da aka kaddamar da shi cikin watan Afrilu, yayin da horaswa ta game-gari, aka fara ta tun 11 Ga Afrilu.

Share.

game da Author