Shekarau ya janye barazanar maka rundunar ‘yan sanda a Kotu

1

Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya sanar da janye shirinsa na maka rundunar ‘yan sanda a kotu kan takardun da aka samu a gidan Sanata Danjuma Goje da yake kunshe da bayanai akan yadda gwamnatinsa ta shirya yadda aka kashe Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam.

A wasikar da Shekarau ya rubuta wa rundunar ‘yan sandan yace dalilin da ya sa yayi hakan shine ganin yadda suke gudanar da bincike akai wanda kuma hakan ya gamsar dashi.

Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya kalubalanci rundunar ‘yan sanada da su binciki maganganu da ake tayi na gano wasu takardu da ya kunshi bayanai akan yadda ya shirya kashe Sheikh Ja’afar Adam a gidan Sanata Danjuma Goje.

Shekarau ya ce yaba ‘yan sandan makonni biyu su gudanar da hakan sannan kuma su sanar da duniya sakamakon binciken nasu ko kuma ya maka su a kotu.

Yace yayi hakanne domin ya wanke kansa daga zargin da ake yi wai an gano wasu takardu da ya kunshi yadda ya shirya kashe Sheikh Ja’afar a gidan Danjuma Goje a samamen da ‘yan sanda suka kai gidansa a Abuja.

“ Wannan bayanai da ‘yan sanda suka fitar akaina ya bata mini suna koma yana iya tunzura mutane suyi mini tawaye. Saboda haka ina rokon rundunar ‘yan sandan da su bada cikakkun bayanai akan ainihin abubuwan da suka samo a gidan Goje.

Shekarau ya roki sifeton ‘yan sanda da ya sa a gaggauta gudanar da bincike akan wadannan bayanai domin ko ya samu ya sha iska ganin yadda akayi masa ca akan wannan bayanai.

A sabuwar wasikar da ya rubuta yau ga rundudunar ‘yan sandan yace ba zai yi hakan ba kuma domin ya na gamsuwa da yadda suke gudanar da bincike akan hakan.

Share.

game da Author