Kwamishinan hukumar kula da aiyukkan zabe na kasa INEC Ahmed Mu’azu yace da taimakon rundunar sojin sama ne suka iya shawo kan matsalar rashin iya tafiyar da aiyukkan rajistan katin zabe a kanan hukumomi biyar a jihar Borno.
Mu’azu ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a Abuja inda ya kuma tabbatar da cewa a yanzu haka ma’aikatan hukumar na tafiyar da aiyukkan su yadda ya kamata a kananan hukumomi 27 a jihar Borno.
Kwamishinan yace sun kasa zuwa kananan hukumomi biyar din ne saboda rashin kyaun hanyar.
Kananan hukumomin sun hada da Damboa, Chibok, Goza, Bama da Kala-Balge.
Shugaban hukumar INEC Mahmood Yakubu ya ce saboda hakan ne ya nemi taimakon shugaban rundunar sojin saman Najeriya Sadique Abubakar domin ya taimaka musu da jami’an sa.
Mu’azu ya ce a yanzu hakan ma’aikatan hukumar INEC na tafiyar da aiyukkan su yadda ya kamata a duk kananan hukumomin kasar harda na jihar Borno.
Da yake tofa albarkacin bakinsa akai Sadique Abubakar ya ce a shirye suke da su taimakawa hukumar INEC din da kuma basu kariya ta musamman domin samun nasara a aikin nasu.