Rundunar Soji ta nada sabon Kwamandan da zai jagoranci dakarun Najeriya a yaki da Boko Haram

0

Kwamandan Askarawan Operation Lafiya Dole, Lucky Irabo yanzu shi ne shugaban Gamayyar Sojojin Hadin Guiwa na Kasa da Kasa, wato Multi-National Joint Task Farce. Haka dai wani bayanin da babbar hedikwatar sojojin kasar nan ya bayyyana a jiya Laraba.

Wanda ya canji Manjo Janar Irabo kuma shi ne Manjo Janar I. Attahiru, a matsayin sabon kwamandan Operatuion Lafiya Dole, a yankin arewa maso gabas.

Wadannan canje-canje su zo ne a daidai lolacin da rundunar askarawan Najeriya ke gudanar da wani gagarimin sauye-sauye a cikin kwamandoji da jagororin kananan rundunonin sojojin a wurare daban-daban.

Babban Jami’in Hulda da Jama’a na askarawan kasar nan, Burgediya Sani Usman, ya bayyana cewa an tura jami’ai 147 a cikin Operation Lafiya Dole, a wasu bangarori da kuma makarantun horaswa na sojoji.

Share.

game da Author