Rikicin PDP: Kwamitin Makarfi na lalube cikin duhu ne, Sherriff ya wuce Tunaninsu – Inji Hon. EJ

0

Dan majalisa mai wakiltar Jihar Edo Hon. AGBONAYINMA a wata tattaunawa da yayi da Mohammed Lere da Nasir Ayitogo na gidan jaridar PREMIUM TIMES’ ya ce kusan duka ‘ya’yan jami’yyar PDP a majalisar wakilai suna bayan Ali Modu Sheriff ne.

Hon. AGBONAYINMA ya ce bangaren Makarfi na lalubene kawai cikin duhu domin ko dokar jami’yyar ta su bata bada damar kafa wata kwamitin riko ba.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su dage da yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu’a addu’ar Allah ya kara masa Lafiya.

PT: Me zaka ce akan rikicin da yake neman hadiye jam’iyyar ku ta PDP wanda hakan ya sa an Samu rabuwar kawunan ‘ya’yan  jami’yyar zuwa bangarori biyu, sannan wace bangare kake?

AGBONAYINMA: Jam’iyyar PDP daya ce kuma shugabanta na asali shine Ali Modu Sheriff.

Shi shugaban rikon kwarya da tawagarsa basu da hurumin kiran kansu shugabannin jam’iyyar bisa ga doka saboda haka ne kaga Ali Modu Sheriff ya sami nasara a kotu. A ganina baza ka taba iya bada abinda baka da shi ba.

Shugaban rikon kwarya da tawagarsa sun rasa yadda za su yi da Ali Modu Sheriff domin tun kafin kotu ta tabbatar masa da shugabancin jami’yyar Ali yake jagorantar jami’yyar.

Idan da sun san shi ba mutumin kirki bane menene amfanin zuwa a roke shi domin ya shigo jam’iyyar sannan kuma ya shugabanceta.

Bai kamata saboda siyasa ba a bata wa Ali Modu Sheriff suna.

Ni dai mai bin doka ne ba mai karya doka ba kuma a bangaren doka na ke. In tare da shi saboda shine shugabana kuma shugaban wannan jami’yyar tamu mai martaba ko anki ko anso.

Babu wanda ya fi karfin doka kuma babu wanda ke da ikon da Allah ke da shi domin Allah ne ya bas hi wannan shugabancin.

PT: Me zaka ce akan daukaka kara da bangaren Makarfi ta kai kotun koli sannan idan suka sami nasara akan hakan me za kuyi?

AGONAYINMA: Bangaren Makarfi sunce idan Sheriff ya sami nasara a kotun koli suna da wata shiri amma mu mun ce idan shi Makarfin ya sami nasara za mu hakura saboda mu masu bin doka ne.

Amma a tsarin mulkin jami’yyar PDP babu wani abu kamar kwamitin rikon kwarya sai dai za a iya samu a kananan hukumomi ko kuma a jiha.

Shi kuma Barista Dayo Adeyeye ya kamata ya na daure tuntuni saboda irin babatun da yake yi idan da muna kasa ce dake bin doka yadda ya kamata.

Abin da ke faruwa shine ita kwamitin rikon kwarya kokari take ta dawo mana da hanun agogo baya misali a zaman neman sulhu da muka yi da bangarensu wanda ya hada da Farfesa Jerry Gana,Sule Lamido da kuma sauransu sun kawo mana wasu manufofi guda bakwai amma muka amince da shida.

Da garin Allah ya waye sai suka ce basu amince da wannan manufofin da suka kawo ba.

Bayan haka suka sake kafa wata kwamitin wanda gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya shugabanta.

Bayan hakan ya faru shine shi kuma gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya ce sam basu yarda ba.

Fayose ba sa’ar Sheriff bane a harkar siyasa. Ina yake lokacin da Sheriff ya yi sanata da kuma gwamna?

Ali-Mak-1

PT: Me zaka ce akan nadin Cairo Ojuogboh yayi?

AGBONAYINMA: Kada ka manta cewa Cairo Ojuogboh shine mataimakin shugaban jami’yyar na yankin kudancin kasa kuma har yanzu shine akan kujeran.

Nada shi da Sheriff yayi bai saba ma doka ba a matsayinsa na shugaban jami’yyar.

PT: Ko zaka iya fada mana suna yen gwamnonin da suke tare da Sheriff?

AGBONAYINMA: Zan dai fada maka gwamnoni uku da basu tare da Sheriff sauran ka lissafo da kanka.

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose da gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo sauran gwamnoni kuwa duk suna tare da Sheriff.

PT: ‘Yan majalisan wakilai nawa ne ke tare da Sheriff?

AGBONAYINMA: A yanzu haka ba mu san adadin yawan su ba domin duk gwamnan dake tare da Sheriff ‘yan majalisan jihar sa suma suna tare da Sheriff.

Bari in gaya maka wani abu, yanzu hakan bangaren Makarfi a rude suke saboda hakan.

PT: Shugaban kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin lafiya a rayayinka na dan jami’yyar PDP kuma dan majalisan wakilai, kana ganin Buhari ya hakura da mulkin ko A’a?

AGONAYINMA: A ra’ayina, ni dan jam’iyyar PDP ne amma kuma kafin hakan ni dan kasa Najeriya ne.

Masu iya magana sun ce mai son abinka ya fi ka dabara. Abin da ya kamata mu yi wa shugaba Buhari shine ci gaba da yi masa addu’a Allah ya bashi lafiya sannan kuma su so junan mu domin shugaban mu ne shi.

Idan shugaban kasa Buhari ya sami nasaran gyaran kasan yadda ya mune za mu amfana da ribar gyaran da ya yi.

Saboda haka a ra’ayina abin da ya dace shine mu kaunaci junan mu kuma mu dage dayi ma shugaban mu Muhammadu Buhari addu’a da sauran shugabanin kasar nan.

tmp_13979-FB_IMG_1493663459121731637691

Share.

game da Author