Jam’iyyar PDP ta ce ba ta ga abin da za a yi wa murna ba a zagayowar ranar demokradiyya na wannan shekara.
PDP tace gwamnatin Buhari bata tsinana wa mutanen Najeriya komai ba in banda tsantsagwaran wahala da ake sha a duk inda ka leka.
Kakakin jam’iyyar na bangaren Makarfi Dayo Adeyeye ne ya sanar da hakan a wata takarda da jam’iyyar ta fitar.
Yace su a jam’iyyar PDP basu ga abin da za ayi wa murna ba a tsawon shekaru biyu da jam’iyyar APC ke mulki a kasa Najeriya.
Ya ba da misalai inda ya kwatanta gwamnatin su da wannan gwamnati na Buhari.
“ A lokacin Mulkin PDP mun tafi mun bar Dala ta na naira N190 amma yanzu Dala ta kai naira N400. Mafi karancin albashin ma’aikacin gwamnati wanda naira N18,000 zai iya siyan akalla buhuhunan shinkafa biyu harda canji amma yanzu ina. Da buhun siminti na naira N1,700 ne amma yanzu naira N2,700 ne. Da dai sauransu.
Bayan haka jam’iyyar tayi magana akan harkar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnati ta sa a gaba sannan kuma tayi kira ga mataimakin shugaban kasa da ya gaggauta saka hannu a kasafin kudi ko a dan samu sauki a wahalhalun da mutane ke fama dashi.