Hukumar Hana Laifukan Harkalla Da Zambar Kudade, EFCC, ta kwace asusun ajiyar kudade na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, NIA a ranar Juma’ar da ta gabata. Hakan ya biyo bayan wani gagarimin bincike ne da aka fara dangane da naira bilyan 13 da EFCC ta bankado a wani gida a Ikoyi, Lagos, kudin da aka hakkake mallakar hukumar NIA ne.
Wadannan makudan kudade da shugaban hukumar Ayodele Oke ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mallakar hukumar sa ce, sun kai ga dakatar da shi daga aiki bayan an kafa kwamitin binciken yadda aka yi wadannan makudan kudade suka je cikin gidan da aka bankado su.
Ana wata kuma sai ga wata, wata majiya ta jami’an tsaro ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata, jami’an EFCC sun tilasta wa daraktan kula da harkokin kudi da mulki na hukumar tsaro ta NIA, ya damka gaba dayan sirrin adadin kudade da bayanan da ke cikin asusun ajiyar hukumar ga wani jami’in soja da ke aiki a ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara a Fannin Tsaro.
EFCC dai ta ce wannan jami’in soja mai suna Burgediya Janar Ja’afaru Mohammed shi ne zai zama jami’i na riko da zai kula da harkar kula da asusun bankin da kuma harkokin kudi na hukumar tsaron ta NIA.
Wannan kwatagwangwama dai ta kai ta kawo ne har ta kai cikin satin da ya gabata, jami’an EFCC sun yi wa wasu jami’an tsaron NIA hudu tambayoyin kwakwaf.
PREMIUM TIMES ta boye sunayen wadannan jami’ai da aka yi wa tambayoyi dangane da harkallar kudade a hukumar ta NIA, saboda bayyana sunayen na su zai iya shafar binciken da ake gudanarwa.
Majiyoyi da dama sun bayyana wa wannan jarida cewa, sau biyu a cikin makon da ya gabata, hukumar EFCC na yin kokarin damka asusun ajiyar NIA a hannnun Burgediya Mohammed, amma sai jami’an NIA su ki ba shi hadin kai.
PREMIUM TIMES ta ji cewa ganin yadda NIA ta ki amincewa da damka ragamar harkokin kudaden hukumar ga Burgediya Mohammed ne ya sa ta gayyaci daraktan kula da harkokin kudade na hukumar, da shi da wasu mukarraban sa guda biyu zuwa ofishin ta. Bayan sun shafe awoyi masu yawan gaske ne su na amsa tambayoyin da aka rika sheka musu, ne aka sake su.
An kuma tabbatar da cewa a cikin makon da ya gabata din, sai da EFCC ta dira a hedikwatar NIA din ta yi wa wasu jami’ai tambayoyi masu zafin gaske.
A ranar Juma’ar da ta gabatan dai ne EFCC ta gayyato daraktan kula da harkokin kudin inda ta tsare shi, tsawon awoyi da dama, inda daga bisani jami’an na EFCC suka dauke shi zuwa hedikwatar NIA din kuma suka tilasta shi ya damka sirrin asusun ajiyar kudade na hukumar a hannun Burgediya Mohammed.
EFCC Ta Yi Katsalandan?
Duk da cewa wannan sabon mataki da ka dauka ya samo asali ne daga bankado zunzurutun kudade har naira bilyan 13 na NIA da aka karkatar aka kimshe a wani gida a Lagos, wasu jami’an tsaro da dama su na dora alamar tambaya a kan irin wannan bincike da su ke ganin kamar katsalandan ne EFCC ta yi a cikin sha’anin hukumar leken asiri ta kasa, NIA din. Su na masu kafa hujja da doka ta 2004 da ta kafa hukumar, wacce su ka ce ta yi nuni da cewa an haramta yi wa NIA katsalandan.
“Sashe na 12(1) na dokar NIA ta 1 da ke cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya ya nuna cewa babu zancen yin katsalandan a harkokin kudin hukumar NIA, haka ba a yarda wata hukuma daga waje ta shiga ta kididdige ko ta yi bincike a asusun ba……”
Wannan doka dai tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar ne ya wanzar da ita a cikin 1999, kuma aka kakaba ta, ta zama doka a karkashin dokar Hukumar Tsaro ta NSA.
Gargadi:
Duk da wannan dokar da aka tanadar, ‘yan Nijeriya da dama sun rika tattauna abin da ka iya zuwa ya zo dangane da binciken asusun hukumar liken asiri ta NIA, wadda ake zargin daga asusun ta ne aka gabji makudan kudaden da aka kimshe a wani gida a Lagos, har naira bilyan 13, wadanda EFCC ta bankado.
Ko a cikin watan Afrilu da ya gabata, sai da tsohon ministan harkokin waje, Farfesa Bolaji Akinyemi ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi taka-tsantsan a kan fallasa hukumar leken asiri ta NIA.
Akinyemi dai ya taba kula da harkokin NIA kafin a dauke hukumar kacokan a maida ta a karkashin ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara a Fannin Tsaro, NSA.
Ba Akinyemi kadai ke da wannan ra’ayin ba, har da Cif Emeka Anyeaku, tsohon Shugaban Majalisar Kasashe Rainon Ingila, wato Commonwealth of Nations.
Sai dai kuma ‘yan Nijeriya da dama na masu ra’ayin cewa bai kamata a ce ba za a binciki ko ma wace hukuma ba ce da aka samu da harkallar makudan kudade har naira bilyan 13 ba.
Kwamitin da shugaban kasa ya kafa a karkashin mataimakinsa Yemi Osinbajo, ya tura jami’ai biyu daga ofishin Akanta Janar na Tarayya, domin su domin su yi filla-filla da asusun ajiyar Hukumar NIA.
Cikin makon da ya gabata dai, wasu jami’ai sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sun damu kwarai dangane da yadda aka yi wa NIA katsalandan wajen afkawa cikin sanin sirrin harkokin kudaden su.
Wata majiyar jikin ofishin Shugaban Kasa ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa tsoffin shugabannin hukumar NIA su uku, sun hadu sun dunguma sun je wurin mataimakain shugaban kasa inda suka yi masa bayanin ra’ayin su.
PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin EFCC, amma ba su ce komai ba, dangane da jawabin da aka nemi su yi a kan wannan kwatagwangwama. Kakakin yada labaran ta, Wilson Uwujaren bai dauki waya ba a lokacin da aka kira shi, haka kuma bai maido amsar sakon tes da aka yi masa ba, bayan da farko ya yi alkwarin zai maida amsa nan take.
Discussion about this post