Gwamnatin Kasar Britaniya ta gargadi Najeriya da kakkausar murya kan rade-radin yi wa gwamnatin Buhari juyin mulki da ya bi gari.
Jakadan kasar a Najeriya Paul Arkwright ne ya fadi haka, inda yace duk wanda yake ganin gwamnati batayi masa ba to sai ya jira lokacin Zabe ya zabi wanda yake so amma maganan juyin Mulki sam bai taso ba.
“Bamu da wata matsaya da ya wuce demokradiya kuma muna tare da Canji. Idan abinda mutane suke so Kenan kuma suka zabe to muma muna tare da su.”
A dalilin haka babban hafsan rundunar Sojojin Najeriya Tukur Buratai ya tsawata wa jami’an soji dasu guje wa cusa kansu cikin hayagagar siyasar kasarnan.
Buratai ya fadi haka ne a wata sako da ya fitar ta ofishin kakakin rundunar sojin Janar Sani Usman.
“Ina sanar muku cewa rundunar soja ta sami rahoton cewa wadansu ‘yan siyasa suna bibiyan wasu manyan jami’an soji domin wata bukata da ya shafi siyasa da shugabanci.
Duk da cewa bai ba da bayanai akai ba ana zaton haka yana da nasaba da rade-radin da ya biye gari cewa rundunar Soji ana shirin yi wa mulkin Buhari juyin mulki.
Yace duk wani jami’in soji da yake da burin shiga cikin harkar siyasa to ya ajiye aikinsa tun yanzu.
Wani babban jami’in Soji ya sanar wa gidan jaridar Premium Times, cewa ya sanar da hakan ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo kuma yayi masa alkawarin ci gaba da samar masa da bayanai akan hakan.
“ Duk wani soja da aka samu yana cusa kansa a hayagagar siyasa ko kuma wani abu makamancin haka, to ya kuka da kansa.”