Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa, ta yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kaurace wa zaman kotun da za a yi gobe Labara, inda za a tautauna batun yiwuwar bada belin tsohon gwaman jijar, Sule Lamido wanda a jiya aka tsare a gidan kurkukun da ke karamar hukumar Kiyawa, a cikin jihar.
Sanarwar wadda Mansur Ahmed, mai kula da shafin yada mufofin Sule Lamido a intanet ya fitar, ta ce PDP ta yi wannan rokon ne domin a kauce wa abin da ta kira “gudun kada a yi wa Sule Lamido wani sharri.”
Daga nan an roki magoya baya da cewa kowa ya zauna a gida ya ci gaba da yi masa addu’ar samun nasara. A jiya ne dai alkalin kotun Majistare ta Dutse ya ce a tsare Sule Lamido a kurkuku har zuwa gobe Laraba.
Idan ba a manta ba, a jiya sai da ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon-tsohuwa suka tarwatsa gungun magoya bayan tsohon gwamnan a kotu.
A dan zaman da yayi yana tsare Sule Lamido ya biya wa daurarru 36 tara. Daurarrun dai dukkan su su na tsare ne a kurkukun garin Kiyawa, da ke cikn Jihar Jigawa. Wata sahihiyar majiya ta shaidawa Premium Times Hausa cewa mutanen sun fito ne daga garuruwa da jihohi daban-daban.
Ya kuma ya ba kowanen su kudin motar da zai kai shi gida.