Obasanjo ya nuna damuwa kan rashin hukunta manyan da suka wawure dukiya kasar nan

0

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana damuwar sa a kan yadda ba a samun nasarar gurfanar da wasu mashahuran da suka wawuri dukiyar Nijeriya.

Ya bayana haka ne a ranar Talata yayin da ya ke gabatar da makala a kan sanin tsarin shugabanci nagari da kuma kalubalen da ya dabaibaye ci gaban Nijeriya: Ina mafita?

Wannan taro dai cibiyar Olusegun Obasanjo ce ta shirya shi, wato cibiyar nazarin kyakkyawan shugabanci da bincike kan tafarkin ci gaban al’umma da ke karkashin Jami’ar da ake karatu daga gida, wato NOUN.

Ya nuna takaicin sa cewa duk da irin yinkurin da gwamnatocin da suka gabata suka yi wajen kokarin hana yaduwar cinnhanci da rashawa, amma har yanzu matsalar ta zame mana babban abin damuwa kuma karfen-kafa. “Rashin nasarar gurfanar da manyan ‘yan siyasar da suka wawuri kudade har a hukunta su, hakan wata matsala ce da ta shafi kasar nan a nan cikin gida, har ma a idon duniya.

Obasanjo ya kara da cewa maimakon a ci gaba da nuna wasu da yatsa ana cewa su ne da laifi, to ya kamata masallatai da coci-coci su bada himma wajen yin wa’azin haramcin wawurar kudin al’umma.

Shi kuwa tsohon shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya ce matsalar shugabancin da Nijeriya ke fama da ita, duk iri day ace da ta Nijeriya, sannan kuma yay i kira ga Nijeriya da ta daure a hada kai Afrika ta Yamma a dunkule wuri guda.

A nasa bayanin, Shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Abdalla Uba Admu, ya bayyana cewa an kafa cibiyar ne a jami’ar sa, saboda ta damu sosai da kalubalen da ke gabanmu na maysalar shugabanci.

Ya ce an sa wa cibiyar sunan Olusegun Obasanjo ne, domin shi ne babban misali na kyakkyawan shugabnci a Afrika gaba daya.

Ya ce rawar da Obasanjo ya taka wajen kokarin sa na dakile cin hanci da rashawa a kasar nan ta hanyar kafa hukumaomin yaki da cin hanci da rasawa. Sannan kuma ya ce NOUN ta yanke shawarar saka sunan Obasanjo ne, domin shi ne ya farfado da jami’ar cikin 2003, bayan watsi da aka yi da ita tun a cikinn 1984.

Ya bada misalan hukumomin da Obasanjo ya kafa da su ka hada da EFCC, ICPC da sauran su. Haka kuma Farfesa Adamu ya kara nuna cewaObasanjo ne kadai shugabann kasar da ya koma ya na karatu a jami’a yayin da yak e a kan mulki, kuma bayan saukar sa ya ci gaba, ga shi a yanzu har ya kai mataki na Ph.D.

Sauran wadanda suka yi jawabai a wurin sun hada da tsohuwar shugaban alkalan kotun kolin Nijeriya, Maryam Aloma Muktar da shugaban cibiyar Farfesa AY Shehu. Taron ya kuma samu halartar mutane da dama, ciki har da shugaban jami’ar na farko da kuma Farfesa Tenebe, wanda ya sauka bayan kammala wa’adin sa Farfesa Abdalla ya karba.

Share.

game da Author