Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa mafi yawan-yawan makiyayan da ke far ma kauyuka da gonakin mutane kasar baki ne wanda suka shigo daga kasashen da ke da iyaka da Najeriya.
Ministan ayyukan noma Audu Ogbeh ne Ya fadi hakan a taron da aka yi a Abuja inda yace gwamantin Najeriya za ta sanarwa kungiyar hadin kan kasashen Afrika AU shirinta akan yadda za ayi wa makiyaya iyaka wajen shigowa kasar ba tare da izini ba.
Jihohi kamar Kaduna, Taraba, Benue da Niger sun yi hasarar mutane da dama dalilin rikici tsakanin makiyaya da manoma a yankunan su.