Ma’aikatar kimiyya da fasaha ta sanar da cewa ta kusa kammala shirin ta na kirkiro maganin cutar farfadiya a kasa Najeriya.
Ministan kimiya da fasaha Ogbonnaya Onu ne ya fadi hakan a taron bita da ma’aikatarsa ta shirya wa ‘yan Najeriya a babbar birnin kasar Amurka wato New York.
Ministan ya kara da cewa a yanzu hakan sun gama yi wa maganin duka gwaje-gwajen da ya kamata domi hakan.
Ya ce yanzu suna jiran hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa Najeriya NAFDAC ta yi nata gwajin akan maganin kafin su kammala sauran abin da ya kamata.
” Muna kokarin kirkiro maganin warkar da cutar farfadiya kuma mun gwada ingancinsa. Muna dai jiran hukumar NAFDAC ta yi kammala nata gwajin akan maganin.’’
” kamar yadda aka sannin cewa cutar farfadiya cutace wanda ta adabi kowa a duniya saboda hakan ya kamata mu hada hannu gaba daya wajen siyar da maganin.”
Onu ya yi kira wa mutanen Najeriya da suke zama a kasar Amurka da taya kasa Najeriya tallata maganin.