Bayan saka baki da tsofaffin shugabannin kasarnan da wasu masu fada aji su kayi kan majalisar jihar Kano ta janye binciken da takeyi wa masarautar Kano da ya hada da kashe kudaden masarautar da sarki Muhammadu Sanusi II yayi batare da bin ka’ida ba, wata sabuwa kuma ta sake bullowa domin hukumar da ta fara bicike akan hakan ta ce tunda majalisar jihar ta dakatar da binciken ita zata ci gaba.
Hukumar Sauraren Koke-koke ta Jihar Kano ta ce dama can duk takardunta na nan a ajiye saboda haka zata ci gaba da aikin ta.
PREMIUM TIMES ta gano cewa hukumar ta samu umarnin kotu da ta bincikin fadar sarkin har sau biyu.
Wani jami’I a hukuma yace tunda majalisar Kano din ta janye na ta binciken akan masarautar Kano su yan zu za su iya komawa su ci gaba daga inda suke tsaya.
Jami’in yace da ma can basuji dadi da majalisar ta ce itama za ta binciki sarkin ba kuma hukumar tana da isassun bayanai akan yadda aka kashe kudaden masarautar bayan umarni da ta samu daga kotu har sau biyu ta ci gaba da bincike akan masarautar.
Da yake zantawa ta wakilin PREMIUM TIMES ta wayar tarho daga birnin Madina, Shugaban hukumar Muhyi Magaji yace dukkan bayanan da suka samo da tun farkon binciken na nan a ajiye babu abin da ya taba su. Y ace sauran bayani sai ya dawo daga aikin umrah.
Da muka leka ofishin hukumar, mun tadda ana ta aiki akan wasu takardu da muke ganin suna daga cikin takardun shaidun da hukumar ta samo kan binciken da tayi tun a baya.