Kungiyar Dattawan Arewa NEF sun nuna goyon bayansu ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayinsa na shugaban Kasa na wucin gadi.
Bayan haka kuma kungiyar ta jinjina wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari da irin namijin kokarin da yakeyi na ganin ya bi yadda dokar kasa ta shimfida musamman wajen mika mulki ga mataimakinsa idan zai bar kasa.
Mataimakin kungiyar Paul Unongo ne ya sanar da hakan da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da kungiyar tayi a Kano.
“ Kungiyar na tare da mataimakin shugaban kasa Osinbajo kuma muna rokonsa da ya ci gaba da yadda yake gudanar da mulki a kasa Najeriya cikin natsuwa da sanin ya kamata da bin tsarin doka.
“ Muna rokon shi da ya toshe kunnuwarsa daga jin maganganun mutanen banza, wadanda za su iya zuwa su fesa masa wata maganar karya da zai iya hada shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Yayi kira ga mutanen kasa da su ba Osinbajo hadin kai domin samun nasara akan abinda ya sa a gaba.
Kungiyar ta yabi Buhari da irin kokarin da yayi wajen ganin an kusa kawo karshen babban matsalar da yankin Arewa take ta fama dashi wato matsalar Boko Haram. Sannan sun yaba wa shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da na Majalisar Dattawa Bukola Saraki kan irin nasu gudunmuwar da suke ba shugaban kasa.
“ Kamar sauran miliyoyin ‘yan Najeriya, kungiyar Dattawan Arewa na yi wa shugaban kasa addu’ar Allah ya kara masa lafiya.
Bayan haka kuma kungiyar ta roki gwamnonin arewa da su gama ayyukan da gwamnonin da suka gabata basu kamala ba a jihohinsu.
“ Muna so muyi amfani da wannan dama domin kira ga gwamnoni da suyi koyi da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje wanda yake ta karisa ayyukan da gwamnonin baya basu gama ba a jiharsa.
“ Muna matukar farin ciki akan hakan da Ganduje yake yi.
“ Kamar yadda wasu gwamnonin suke ta kokarin fara sabbin ayyuka, shi Ganduje kokari ya ke ya kammala wadanda ya gada da wadanda gwamnonin da suka gabata suka bari basu karisa ba.
Kungiyar tace yanzu haka tana zazzagayawa jihohin arewa ne domin ganin abubuwan da ke faruwa da kuma bada shawarwari akan abinda suka ga ya dace ayi.