TAMBAYA: Shin da gaskene ahlussunna zai iya shan rubutu ko ya rike laya?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Shan Rubutu
Ya halatta Musulumi ya sha rubutu a shari’ance. Domin Al-kur’ani waraka ne ga zuciya da ganganjiki. Al-kur’ani ya ce “muna saukar da waraka a cikin Al-kur’ani” kuma Annabi SAW ya ce “Alkur’ani shi ne mafi-ficin magani”.
Ana iya rubuta wani bangare na Al-kur’ani, a allo na katako ko na karfe, gilas, takarda ko dukkanin wani abin rubutu mai tsarki da tawadar Za’afaran ko dukkanin wata tawada mai tsarki. Sannan a wanke da ruwa mai tsarki.
Sahabai da sauran magabata sun koyar da haka don bada taimako ga:
1. Mara lafiya
2. Mace Mai nakuda
3. Mai Aljani
Za’a sha rubutun ko a shafa a jiki ko ayi wanka da shi.
Sharuddan Shan Rubutu
1. Tsarki: a rubuta da Alkalami me tsarki, Tawada me tsarki kuma a kan
abu me tsarki.
2. Tsafta: Rashin cutarwa ga jikin dan adam.
3. Rubutun kuma ya kasance rubutu ne me karantuwa ga kowa.
4. Dole ne abinda aka rubuta ya zama Al-kur’ani ko addua, ko sunayen Allah.
Masana sun tabbatar da amfanin yin magani da ayoyin Allah da kuma tsananin tasirin sa wajen dacewa da samun waraka.
Amma fa duk da haka, malamai sun ce abinda yafi dacewa da sunnan Manzo SAW shi ne:
1. A karanta Al-kur’ani a tofa a jikin mara lafiyan, ko
2. A karanta Al-kur’ani a tofa a cikin ruwa, mara lafiyan ya sha ko ya shafa, ko
3. A dafa gurin da ke ciwo a jikin mara lafiya, sannan a karanta Al-kur’anin, ko
4. Ayi rukiya da Alkur’ani ga mara lafiya.
Rike Laya
Dukkanin Malamai magabata da ‘yan baya sun yi ittifaki akan haramcin rike layar da aka yi ta ba da Alkur’ani ba, ba da sunayen Allah ba, kuma bada kyak-kyawan addu’a ba. Kuma sun da ce akan cewa yin hakan shirka ne kuma laifi ne mai girma.
Amma kuma Malaman sun yi sabani a kan Mas’alar rike layar da akayi da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a. Fatawar su ta kasu zuwa gida uku a kan Mas’alar rike layar da akayi da Alkur’ani, sunayen
Allah ko kyak-kyawar addu’a, kamar haka:
1. Jamhurin Malamai (mafiya rinjaye) sun tafi akan hallacin rike layar da akayi da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a, tare da gindaya wasu ka’idojin da za mu ambata.
Mafiya rinjaye daga gawurtattun malamai, kamar malaman duniyar Malikiyya, Shafi’iyya, Hambaliyya, da Hanafiyya duk sun halatta daura layar Alku’ani dogaro da wasu ruwayoyi na manyan magabata kamar Nana-Aisha R.A, Abdullahi Dan Amru R.A da Sa’idu Dan Musayyib da sauransu.
Layar da malaman su ke ganin ta halatta dole ne ta kasan ce:
I. Wani bangare ne na Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a.
II. Me tsarki, akan abu me tsarki, kuma a rufe ta a cikin abu me tsarki.
III.Ana nufin tabarruki da zikirin da ke cikin layar.
IV. Akan yakinin cewa Allah shi ne mai warkarwa, mai karewa ba layarba.
V. Rubutun kuma ya kasance rubutu ne me karantuwa ga kowa babu surkulle a ciki
2. Wasu malaman kuma sun karhanta (sun kyamaci) rike layar da akayi da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a.
Manyan magabata kamar Alhassan Albasari da Ibrahim Ibn Muhajir sun kyamaci rike layar da aka yi da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a, ko ingantacen zikiri.
3. A wani bangaren kuma wasu malaman ne suka haramta rike laya ko wace iri ce.
Malamai kamar su Ibn Bazz, Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahhab da riwayar hadisai na Ibn Mas’ud da Imam Ahmad sun haramta rike laya ko wace iri ce sabo da fadin Manzo SAW “ duk wanda ya rataya laya to, ya yi shirka”.
A karshe, Allah ya shiryar da ku, ahlussunna zai iya shan rubutu ko ya rike laya, matukar yanada yakinin cewa waraka daga Allah ne, shi ne me karewa, kuma me warkarwa. Sannan ya kudur ce a zuciyarsa cewa shan rubutun da rike layar donin neman albarkar da ke cikin ayoyin ne, ko sunayen Allan ne ko kuma addu’ar ne.
Imam Muhammad Bello Mai-Iyali, Cibiyar yada Addinin Musulunci na Harakatu Falahil Islam Barnawa Low – Cost, Kaduna.