A dan kwanakin nan mazauna jihar Kaduna na fama da tashin hankula dabam dabam da ya shafi musamman ayyukan matasa wadanda akafi sani da ‘yan Shara.
Duk da cewa gwamnatin jihar tana kokarin ganin ta kawo karshen ayyukan wadannan matasa a jihar abin dai da kamar wuya domin yana wuya baka ji tashin hankali na irin wadannan matasa a wasu sassan jihar ba kusan kullum ko dan bayan kwanaki.
Unguwannin da sukayi kaurin suna da ayyukan irin wadannan matasa sun hada da Badarawa, Kawo, Unguwan Rimi, Kakuri da Sabon Tasha.
A wadannan unguwanni yana wuya a yi kwanaki 10 bakaji wai an sari wani da makami ba ko kuma wadansu sun kai ramuwar gaiya wasu unguwanni da suke zaman gaba a tsakaninsu.
Wani Mazaunin unguwan Badarawa Majalisa Hamza Mi Kifi ya sanar mana cewa unguwan yanzu ya fara fin karfin mazauna domin ayyukan yaran yana neman ya hana mutane gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
“ Zai yi wuya ace wai an shafe makonni biyu cur baka ji yaran unguwa sun fito suna sare-sare ba a titunan unguwan. Za ka ga mutane na ta gudu wasu na zubar da kayan sana’arsu a duk lokacin da hakan ke faruwa.
“ Duka yaran baza su wuce ‘yan shekara 17 zuwa 25 ba. Duk da cewa jami’an ‘yan sanda na zuwa suyi kame bayan haka amma ba a dadewa zaka ga irin wadannan yaran a gari suna gudanar da harkokinsu.
Mafi yawa daga cikin mazauna unguwannin nan da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA sun koka da gata da iyaye suke nuna wa ‘ya’yansu.
“ Za ka ga uba yana kare dansa bayan ya san dan sa bashi da gaskiya.” Inji wani magidanci a unguwan Kawo.
A wadannan unguwanni a na samun matsalolin gaske da irin ayyukan wadannan matasa.
Wata Mazauniyar Unguwan Sabon Tasha Grace John ta ce a kwai wani layi da ake kira ‘Black Street’ a unguwan babu irin ta’addancin da matasan wannan layi basa yi.
Tace baka is aka bi wadannan layuka ba da daddare.
A Kakuri da Unguwan Rimi ma abin dai kusan daya ne. Duk wadanda muka zanta dasu suna kokawa da ayyukan matasannan yankin.
“ Ka gani a Unguwar Rimi, abin ya dan lafa domin gwamnati ta danyi maganinsu, amma ina gaya maka har yanzu ana fama da ayyukan wadannan yaran. Wasu lungunar ba zai biyu maka ba domin tabbas zasu yi maka lahani da makami.
“Rashin hukunta yaran nan yadda ya kamata ne sannan kuma da yaro ya san idan ya aikata wani laifi za a iya kama ubansa a madadinsa a hukuntashi da su kansu iyayen basa daure ma ‘ya’yan gindi.
Kira ga Gwamnati
Duk da cewa kusan duka mutanen da muka zanta da su sun yabi gwamnatin jihar da yin namijin kokari wajen ganin an kawo karshen ayyukan irin wadannan matasa sun roki gwamnati da ta kara bada himma akan ganin wadannan yara basu zama abin da za ayi da na sani ba nan gaba.
Wani Malamin addini, Mohammed Auwal ya dangana laifin lalacewar ‘yaya ga iyaye sannan kuma ya koka da yadda jami’an tsaro suke sakin wadanda aka kama ba tare da an hukunta su ba yadda ya kamata.
“ Sau da yawa zaka ga iyaye ne ke nuna halin ko in kula da yadda ‘ya’yansu ke tafiyar da al’amuransu a unguwannin mu. Wani dan ma ba’a san yadda yake rayu ba sannan kuma idan ya jajibu wata fitinar sai kaga ubane ke kan gaba wajen kare shi. Bayan kuwa za a tambayi kowa yadda ya kiwata abinda Allah ya azurtashi da su domin hakan ya hada da ‘ya’yan mu.
Mal. Auwal ya ce suma jami’an ‘yan sanda su dinga hukunta yaran idan har aka kama mutum da laifi wanda hakan zai sa na baya su shiga taitayinsu.
James Aboki, wani shugaban al’umma a unguwan Sabon Tasha ya yi kira ga gwamnati da ta mai da hankalin ta kan ayyukan wadanan yara domin abin ba yadda suke ji bane yake faruwa.
“ Wadannan abubuwa sun fara zama ruwan dare a Kaduna domin kusan duk inda kashiga za ka ji ana irin wadannan maganganu akan yara sun sari wancan sun kwace ma wancan kaza da dai sauransu.
“Muma a unguwan nan akwai inda baza ka wuce da daddare ba sai ko a doke ka ko a ji maka rauni sannan a kwace maka dukiyarka.
Bincike da muka yi ya nuna cewa tabbas gwamnati a jihar Kaduna sai ta kara sa ido da daukar matakai domin shawo irin wadannan ayyukan matasa da ke addabar mutanen gari.
Sau da yawa zaka ga sai yaran sun gama cin karensu ba babbaka sannan jami’an tsaro suke tahowa kame unguwannin da abin ya faruwa.
Yaran sukan fito ne dauke da muggan makamai kuma duk wanda yace zai hanasu sai sun yi masa illa.
Wadannan unguwanni na bukatar gwamnati ta kawo musu dauki domin kamar yadda muka jiyo daga mazauna wadannan unguwanni abin kara gaba ya keyi ba baya ba.
Wasu da daga cikin mazauna unguwannin da suka tattauna da mu sun yaba ma gwamnan Jihar Nasir El-Rufai kan yadda ya ke kokarin ganin an kawo karshen irin wadannan ayyuka na matasa sanna sun rokeshi da ya kara baza jami’an tsaro a wadannan unguwannin musamman wadanda aka san ana irin wadannan tashin-tashina.
” Ka duba abinda ya faru a Kabala West, duk daga irin haka ne ya kai ga abin ya kusa ya koma na addini. Badun gwamnati ta yi hubbasa ba da abin ya zama wani abu.” Inji Sani Ikon Allah.