Matasan da suke shirin N-Power sun koka da rashin samun alawus a jihohin Nasarawa da Ekiti

0

Daruruwan matasa ne suka fito titunan garin garin lafiya, Jihar Nasarawa domin gudanar da zanga-zangar neman gwamnati ta biya su kudaden aalwus dinsu har na tsawon watanni biyar.

Matasan sun yi tattaki ne daga shataletalen bankin UBA zuwa sakateriyar jihar.

Jagorar matasan Abdulkareem Isiaka yace dayawa daga cikin matasan basu sami alawus dinsu ba har na tsawon watanni biyar.

“ Mun kai kukan mu kananan hukumomin da abin ya shafa basu ce komai ba a kai shine yasa muka fito gaba dayan mu ko gwamnati za ta share mana hawaye.

A jihar Ekiti ma sama da mutane dubu daya ne suka fito domin gudanar da irin wannan zanga zanga.

Masu zanga zangar sun koka da rashin biyan su alawus har na tsawon watanni shida.

Suma sun kai kukansu ofishin N-Power dake jihar.

Share.

game da Author