Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta gana da ‘yan matan Chibok

0

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta gana da ‘Yan natan Chibok da aka sako makon da ya gabata.

A tawagar Aisha, akwai uwragidan mataimakin shugaban kasa Dolapo Osinbajo da matan gwamnonin wasu jihohin kasar.

Aisha ta jinjina wa gwamnati kan irin namijin kokari da tayi wajen kwato ‘yan matan da sukayi kusan shekara uku suna tare da Boko Haram.

Ta yi kira a garesu da su kwantar da hankalinsu su sannan suyi shirin komawa makaranta domin ci gaba da kara tunsu.

Itama Dolapo Osinbajo ta roki ‘yan matan da su manta da abinda ya faru dasu a baya.

Share.

game da Author