‘Yan siyasa a kasa Najeriya sun fara shirin tunkarar 2019 a bangarori dabam dabam na kasa Najeriya.
A jihar Adamawa magoya bayan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar da na tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso sun goge raini inda har wasu da yawa sun sami raunuka da dama a jikkunansu.
Wani mazaunin garin yace mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya shirya hakan domin rikicin ya faru ne bayan Atiku ya iso wajen da za’ayi nadin sarautar da magoya bayan yan siyasan duka suka taru.
Yace magoya bayan Atiku sun lakada wa duk wani da suka gani da jar Hula inda a yanzu hakan mutane 10 na kwance a asibiti.
Y ace sun sami labarin cewa an dauko hayar yan daba ne daga jihar Bauchi domin su zo su ci wa magoya bayan Kwankwaso mutunci a garin.
Mai Magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe ya karyata wannan zargi na magoya bayan kwankwaso. Ya ce Atiku bashi da wata masaniya ko hannu a abin da ya faru a jihar.