Lallai giyar mulki ta fara bugar da Garba Shehu; Me ya sa gwamnati taki bin umarnin kotu kan El-Zakzaky – Femi Falana

0

Babban lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya soki lamirin Babban Mai Taimaka Wa Shugaba Buhari a Fannin Yada Labarai dangane da kalaman da ya yi a kan dalilan da su ka sa har yanzu gwamnati ke tsare da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Falana, ya fada a cikin wata takardar da ya aika wa kafafen yada labarai a ranar Laraba cewa irin wadannan maganganu marasa hujja bai dace su na fitowa daga bakin Garba Shehu ba.

Ya ce wannan ne karo na farko a tarihin kasar nan da gwamnatin farar hula wacce talakawa su ka zaba, amma a wayi gari ta na amfani da doka irin ta mulkin soja da aka taba kuntata wa ‘yan Najeriya da ita wato Decree no.2 ta 1984. Abin mamakin kuma shi ne, ba sau daya ko sau biyu ba kotu ta ce a saki El-Zakkazy, amma gwamnati ta take umarnin kotu.

“Amma abin mamaki, sai ga shi a yanzu ana mulkin dimokradiyya, babbar kotun tarayya ta ce tsare El-Zakzaky babban laifi ne, shi kuma Shehu ya ce an tsare shi ne saboda hali na tsaro ko kuma saboda tsarewar ta fi zama alfanu ga malamin da ke tsare.”

“Tabdijan! Wato ashe har giyar mulki ta fara bugar da Shehu yadda zai fito kiri-kiri ya na take umarnin kotu, kuma babbar kotun tarayya?” Inji Falana.

Shehu dai ya ce ba a kurkuku ne ya ke a tsare ba, ya na a killace tare da matar sa da kuma ‘ya’yan sa. A kan haka ne Falana ya ce jawabin Shehu ya ci karo da jawabin da fadar shugaban kasa din ta taba yi cewa tsare El-zakzaky tilas ne domin sakin sa zai iya zama barazana ga hukuma.

“Shin wai Shehu bai san cewa El-Zakzaky ya rasa idon sa daya ba ne a hannun jami’an tsaro? Kuma zai iya rasa dayan a ci gaba da tsare shi da ake yi saboda an hana shi ya fita ya nemi magani?”

Me ya sa aka ki amincewa da rokon da ya yi a bar shi ya fita waje domin ya nemi magani?

Daga nan sai Falana ya yi kakkausan kira da a gaggauta sakin El-Zakzaky da Sambo Dasuki wadanda ake ci gaba da tsare su duk kuwa da kotuna sun sha bada umarnin sakin su, amma gwamnati ta yi biris da umarnin kotun.

Shi dai El-Zakzaky ya na tsare ne tun cikin watan Disamba, 2015 tare da matar sa Zeenat, bayan hargitsin da ya faru a Zariya, inda sojoji suka bude wa mabiyan sa wuta, aka kashe sama da 300, ciki kuwa har da ‘ya’yan sa, da mataimakin sa, Sheikh Turi.

Share.

game da Author