Kungiyar FOMWAN tayi kira ga gwamnati da ta kara wadata fannin kiwon lafiya da kudade

0

Kungiyar mata Musulmai na FOMWAN ta yi kira ga gwamnati da ta kara yawan kudaden da take ware wa fannin kiwon lafiya a kasafin kudin kasa.

Shugaban kungiyar na reshen babban birnin tarayya Abuja, Maryam Aliyu ta roki gwamnati da ta mai da hankali wajen wadata fannin kiwon lafiya da kudaden da ta ke bukata domin samun nasara akan abinda ta sa a gaba na taimakawa marasa lafiya da ta keyi.

Maryam ta fadi hakanne a fadar sarkin Abaji Adamu Yunusa inda ta nuna cewa yin hakan zai taimaka wajen kawar da cututtukan da suka addabi mutane musamman na karkara da ya hada da cutar kwalara,cutar sanyin hakarkari wato pneumonia, yin rigakafi akan lokaci, tabbatar da cewa yara sun sami abincin da zai gina musu jiki da hikimar da ke tattare da bada tazarar haihuwa.

Mai martaba sarkin Abaji a nashi tsokacin ya nuna farin cikinsa da ziyarar da kungiyar ta kawo fadarsa sannan kuma ya jinjina musu kan irin kokarin da suke yi na taimakawa marasa lafiya a kasa baki daya.

Share.

game da Author