Kungiyar bada tallafi na duniya zata ci gaba da taimaka wa fannin kiwon lafiya na Najeriya

0

Asusun bada tallafi na duniya ‘Global Fund’ ta ce za ta ci gaba da tallafawa fannin kiwon lafiyar kasa Najeriya musamman bangaren da ya shafi bada magunguna, kudade, taimako domin gunnar da bincike da kuma tsarin da zai kawo ci gaba wajen yaki da cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro da kuma tarin fuka.

Ma’aikatan kiwon lafiya ta kasa ne ta sanar da haka a taron kiwon lafiyar duniya na karo ta 70 da aka yi a Abuja.

Kamar yadda aka sani cewa shugabanin ma’aikatan kiwon lafiya da suka gabata sun yi watanda da kudaden tallafin da ake samu daga kungiyoyi masu zaman kansu da kuma asusun bada tallafi na duniya.

Hakan ne ya sa wasu kungiyoyin da suke tallafa wa fannin kiwon lafiyar kasa Najeriya suka dakamar da ci gaba da bada tallafin da suka saba bayarwa.

Shugaban asusun bada tallafi na duniya Mark Dybul ya ce sun amince da yin hakan ne saboda irin gaskiya da ministan kiwon lafiya Isaac Adewole yake da shi.

‘’Saboda gaskiyarka da sanin ya kamata da ke kwatantawa wato shi minista Adewole a aikinka da kuma rokon alfarmar da ka yi yasa baza mu rage tallafin da muke ba fannin kiwon lafiyar kasar nan ba sannan kuma ina fatan da zaran nayi ritaya zan iya taimaka wa kasa Najeriya ta hanyoyin da suke bukata’’.

Daga karshe Isaac Adewole ya yi kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su hada kawance da gwamnatin Najeriya domin samarda tallafi ga fannin kiwon lafiyar kasar.

Share.

game da Author