Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya karyata maganan da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo yayi wai shine ya fara aikin ruwan Zariya kafin a nada shi mataimakin shugaban kasa.
A jawabin mataimakin shugaban kasa Wanda John Oyegun da ya wakilci ya Karanta ya ce mutanen yankin sun fi shekara 16 suna wahalar ruwan sha sai gashi jam’iyyarsu wato jam’iyya mai ci APC a karkashin gwamna El-Rufai ta kammala aikin cikin shekaru biyu kacal.
A nashi jawabin Namadi Sambo ya yabawa gwamna El-Rufai sannan kuma ya ce ko da ma can an sami aikin a kan gaba ne aka ci gaba daga inda ya tsaya.
Mutanen Zariya da suka tattauna da gidan jaridar Premium Times Hausa sun jinjina wa gwamna El-Rufai kan ganin wannan aiki ya tabbata a zamanin mulkinsa.
” Wannan abin farincikin da ya same mu ba za mu ta ba mantawa da shi ba. Ni dai na shekara 40 amma gaskiya Duk da ba zama nakeyi ba a garin amma ban taba ganin ruwan famfo a Zariya ba in ba na rijiyar burtsate ba amma wai ka bude famfo ka ga ruwa sai dai kila daga yanzu.Mu fa El-Rufai yayi mana komai.” Inji Umar Mohammed
Gwamna El-Rufai ya ce gwamnati zata ci gaba da aiki a sashen matatar ruwar na biyu.