Kotun majistare da ke jihar Jigawa ta ba da belin tsohon Gwamnan jihar, Sule Lamido, wanda ake zargi da laifin tunzura magoya bayan jam’iyyarsa ta PDP da suyi wa gwamnatin jihar bore a lokacin zaben kananan hukumomi.
Kotun ta bayar da belinsa yau a garin Dutse san nan ta tsayar da ranar 5 ga watan Yuli domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa, ta yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kaurace wa zaman kotun yau saboda gudun kada ayi amfani da taron magoya bayan tsohon gwamnan ace wai ya aikata wata laifin.
Mataimakin sufritandan ‘yan sanda mai kula da bincike ya ce ‘yan sandan sun tasa keyar Sule ne bayan kukan da gwamnatin jihar ta kawo gabanta cewa gwamnan ya umurci magoya bayansa da su ta da hankalin jama’a a zaben kananan hukumomi da za’ a yi a jihar nan bada dadewa ba.
Sule ya ce ” Kafin wannan zabe sai na tabbatar kowani daya daga cikinku ya yi mini rantsuwa da rayuwansa akan wannan abu da muka sa a gaba.
” Ko ma menene ya faru ba zan saurari kukan ku ba. Abin da nake so kawai Inji shine an nemeni da inzo in bada belin kowani dayanku don ko kun fasa ma wani kai ko kuma kun yi ma wani jina-jina domin wannan gwamnatin mahaukata ce.