Sakamakon korafe-korafe da aka rika yi, tun bayan da Premium Tmes ta buga labarin korar dadaddun ma’aikatan ta 200 da kuma wasu ma’aikatan wucin-gaci su 80, kamfanin MTN ta bayyana dalilan da ya sa aka salami ma’aikatan dga aiki.
Idan dai za a iya tunawa, MTN ta ba ma’aikatan ta 280 takardar sallama, daga cikin ma’aikata 1800 da ta ke da su a nan Nijeriya. Wadanda aka sallama din sun fito ne daga bangarori da matakai daban-daban har ya zuwa wasu manyan manajojin kamfanin.
Sai dai kuma jami’in yada labaran MTN, Funso Aina, ya bayyana cewa sallamar ma’aikatan ta biyo bayan wani gagarimin garambawul da kamfanin ya fito da shi, inda suka ga cewa akwai bukatar a sallamik tsohuwar zuma domin a samu kai wag acin wani zango da kamfanin ke zo ya kai nan da wani karamin lokaci.
Ya kuma tabbatar da cewa duk wanda aka sallama, tun ma kafin a sallame shi ya riga ya sani, domin an zauna da shi an sanar da shi kalubalen da ake son kaiwa, kuma sai da aka tuntubi na gaba da su da wadanda suka tsaya musu wajen samun aiki.
Ya kuma ce ba a bar dukkan wadanda aka sallama din sun tafi hannu biyu ba.