Wasu ‘yan Najeriya sun yi kira ga Buhari da ya dauki dogon hutu domin nema wa kansa lafiya.
Babban lauya Femi Falana da wadansu manyan ‘yan Najeriya ne sun roki Shugaban kasa da ya bi shawaran likitocinsa ya dauki dogon hutu domin nema wa kansa lafiya da samun hutun da jikinsa ke bukata.
Sun ce fadar shugaban kasa ta dade tana boye-boye kan matsayin lafiyar shugaban kasa amma kuma ga dukkan alamu da irin rahotannin da suke samu ya na nuna cewa Buhari bashi da lafiya.
” Kwanakin baya gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi kira ga masu zuwa wajen Shugaban kasan da su dai na zuwa domin yana bukatan hutu. Haka kuma mako biyu kenan bai fito zaman majalisar zantaswa ba kuma bai iya fitowa Sallar Juma’ar da ta wuce ba.”
Sun roki fadar Shugaban kasan da su daina boye-boye akan halin rashin lafiyar Shugaban Kasar sannan sun roke shi da ya dauki hutu.
Wadanda suka sanya hannu akan wannan kira sun hada da
Farfesa Ibrahim Jibrin, Debo Adeniran, Chris Kwaja, Y. Z. Ya’u, Chom Bagu, Olanrewaju Suraju, Ezenwa Nwagwu, Anwal Musa Rafsanjani, David Ugolor, ‘Sina Odugbemi, Muhammed Attah da Adetokunbo Mumuni.