Kungiyar gwamnonin Najeriya ta karyata rahoton wasu jaridun kasa wai gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari kuma shugaban kungiyar ya gina Hotel da ya kai Dala miliyan 3 a jihar Legas.
A bayanan da gidajen jaridun Nation da Saharareporters suka wallafa sun ce sun sami bayanai na sirri akan haka ne ta hukumar EFCC.
Jami’in dake kula da ayyukan yada labarai da hulda da Jama’a na kungiyar Abulrazaque Barkindo, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ya karyata wannan magana in da ya dangatata da neman ci wa gwamnan mutunci ta hanyar yi masa irin wannan kage amma “bai mallaki koda fili ba ballantana Hotel a jihar Legas.”
” Wannan magana sam bashi da tushe ballantana asali duk da cewa a rahotanni jaridun sun ce wai sun gano hakanne ta dalilin wasu bayanan sirri da suka samo daga EFCC.
” Sun ce wai wasu jami’an hukumar EFCC suka gano wannan hotel da Yari yake ginawa wanda da kudin jihar Zamfara ne na bashin ‘Paris Club’ yayi amfani da su.
” Abdulaziz Yari baya gina wata Hotel a Legas sannan kuma ba shi da wata masaniya akan wadannan batu.”
” Irin wadannan labarai da ba a tantancewa kafin a sanarwa Jama’a ya na cutar da aikin jarida musamman a kasa Najeriya.
Abulrazaque Barkindo yayi kira ga kamfanonin jaridun kasa Najeriya da su dinga yin bincike da tabbatar da sahihancin labarai kafin su wallafa a shafunan jaridun su.