Kimanin jihohi sha hudu a Najeriya ne bincike ya nuna cewa duk cima-zaune ne, kudin shigar da suke samu a jihohin su, bay a iya ciyar da su. Musamman ma a cikin 2016, bai ma kai kashi 10 cikin 100 na kason da su ke samu daga lalitar gwamnatin tarayya ba.
Rahoton da ASVI ta fitar ne ya tabbatar da haka, ya ce jihohin sun hada da Jihar Barno, Ebonyi, Kebbi, Jigawa, Yobe, da Gombe. Akwai kuma wadanda suka hada da Ekiti, Katsina da Sokoto.
Rahoton ya nuna cewa jihar Lagos ce ta fi kowace jiha karfin samun kudin shiga na ta na kashin kanta, har ma ya fi abin da ta ke samu daga kason lalitar gwamnatin tarayya nesa ba kusa ba, inda a 2016 ta samu naira bilyan 302, wato sama da kudin shigar da jihohi talatin ke samu a matsayin kudin shiga, ciki kuwa har ma da jihohin Ogun, Rivers, Edo, Kwara da Delta.