Gwamnatin jihar Gombe ta dakatar da yi wa wasu ma’aikatan jinya da ma’aikatan unguwan zoma guda 100 ritaya saboda karancin ma’aikatan kiwon lafiyar da jihar ke fama da shi.
Shugaban ma’aikata na jihar Daniel Mohammed ne ya sanar da hakan da yake bada jawabinsa a taron zagayowar ranar ma’aikata.
Daniel Mohammed ya ce adadin yawan mutanen jihar Gombe ya kai miliyan 3 sannan tana da yawan ma’aikatan asibitin da suka kai 1159 kawai.
Ya kuma kara da cewa saboda hakan ne ya sa gwamnatin jihar ta dakatar da yi wa ma’aikatan da suka cancanci a yi musu ritaya har sai ta horar da ma’aikatan da za su maya gurbinsu.
“Dakatar da yi wa ma’aikatan asibiti ritaya ya kubutar da jihar shiga cikin wata babbar matsala.”