Jaruma ‘yar wasan fina-finan Hausa, Jamila Nagudu ta sanar da zama sabuwar jakadiyar Kamfanin Vedan masu sarrafa sanadarin abinci mai suna Vedan.
Jamila ta sanar da haka ne a shafinta na Instagram a makon da ya gabata.
A sakon nuna farincikinta kan haka ta godewa Ali Nuhu saboda gudunmawar da ya bata don samun wannan aiki.
” Alhamdullilah yanzu na zama jakadiyar kamfanin Vedan kuma ina nuna godiyata ta musamman ga sarkin farfajiyar fina-finan Hausa Ali Nuhu.”