Mutanen karamar hukumar Shagari a jihar Sokoto sun yi fama da iskar guguwa inda a ta dalilin hakan ne mutane uku suka rasa rayukansu ranar Litini.
Hukumar NEMA ne ta sanar da hakan yau a garin Sokoto.
Shugaban hukumar reshen jihar Sokoto, Sulaiman Muhammad ya ce guguwar ta rusa gidaje 46 a karamar hukumar Shagari da gidaje 93 a karamar hukumar Tambuwal amma babu wanda ya rasa ransa sai dai wasu hudu sun sami raunuka a karamar hukumar Tambuwal.
“ Gidadje sama da 1000 ne wannan iska da ya zo da karfi ya lalata duk da cewa hukumar NEMA din na ci gaba da amsar bayanai akan sauran in da abin ya shafa. Zamu ku tabbatar da cewa mun wadata wadanda wannan ibtilai ya afka wa.”