Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta sa kafar wando daya da Intels, babban kamfanin da Atiku ke takama da shi

1

Wani kazamin rikicin huldar cinikayya ya barke, tsakanin Hukumar Kula Da Tashoshin Ruwa, NPA da kuma kamfanin Integrated Logistics Services, Nigeria Limited, wanda aka fi sani da suna Intels, mallakar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Intels na daya daga cikin manyan kamfanonin da ke huldar kasuwancin man fetur da kuma gas a kasar nan.

Rikicin ya yi muni har hukumar NPA ta yi barazanar soke kwangilar karbar haraji da Intels ke tafiyarwa ko gudanarwa a tashoshin jiragen ruwa. PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da wannan rikicin da kuma barazanar soke kwangilar.

Wadanda ke da masaniyar wannan rikici sun tabbatar da cewa bangarorin biyu sun sha zama a kan teburin shawarar sasantawa, amma ana tashi baram-baram, bayan kowane bangare ya fesa wa kowa zafafan kalamai a wurin taron.

Bayan wannan an kuma sha yin karakainar aika wa juna wasiku dauke da kakkausan kalamai, dangane da zargin rashin bin ka’idojin gwamnatin tarayya na zuba kudi a Tsarin Asusu Daya Tilo, wato TSA.

Wasu takardun wasikun da aka rika aika wa juna, wadanda PREMIUM TIMES HAUSA ta ci karo da su, sun nuna bangarorin biyu sun kasa cimma amincewa matsaya daya dangane da daukar nauyin wasu manyan ayyuka da Intels ke yi wa NPA.

Atiku ne da wani Baturen kasar Italiya mai suna Gabriel Volpi suka kafa Intels a cikin shekarun 1980.

Kiki-kaka A Kan Raba Riba Da TSA

A ranar 15 Ga Maris, Manajar Daraktar NPA, Hadiza Bala Usman, ta rubuta wa kamfanin Intels wasika cewa ta na so kamfanin ya rika aiki da sharuddan raba ribar aikin tara kudin haraji ta hanyar zuba kudaden a Asusu Daya Tilo na Babban Bankin Tarayya, CBN, maimakon a rika zuba kudaden a bankunan ‘yan kasuwa.

A cikin wasikar ne Hadiza ta tsara sabon sharadin raba riba tsakanin NPA da Intels. Ta ce kamfanin Intels zai rika daukar kashi 28 bisa 100 na ribar a matsayin ladar kamasho.

Sauran kashi 72 na ribar za a sake raba shi gwamnati na da kashi 30: yayin da Intels zai dauki kashi 70.

Shi dai tsarin Asusun Bai Daya na TSA, an shigo da shi ne domin a rika tara duk wasu kudaden shiga da gwamnati ke samu a cikin asusu daya, yadda za a hana wawura da karkatar da kudade.

Sai dai a gefe daya kuma ana kuka da tsarin domin hakan na hana yawaitar shigar kudade a cikin asusun da ke karkashin bankinan ‘yan kasuwa.

Amma a ranar 27 Ga Maris, Intels ya maida amsar wasikar shugabar NPA, sai dai duk da ya amince da sabon tsarin raba ribar, sai dai kuma ya ce ba zai iya amince zuba kudade a asusun TSA ba, saboda akwai bankunan da ke bin kamfanin bashi. Tilas zai rika zuba musu kudi kenan. Haka kamfanin ya rubuta a cikin wata wasika da ya aika wa Hadiza Bala Usman, tare da cewa bankunan sun karbi takardun su ne a bisa sharadin za su rika zuba ajiyar kudaden su a cikin bankunan.

“Ke ma kin san bankunan da Intels ke mu’amala da su, ba za su yarda mu rika zuba kudi a Asusun TSA da ke CBN ba.” Haka Babban Shugaban Intels Andrew Dawes ya rubuta wa Hadiza, inda ya kara cewa, “ai idan mu na yin haka, za mu kasance babu ko sisi a hannun mu da za mu rika gudanar da ayyuka. Hakan kuma mun tabbatar NPA ba za ta so ya faru ba.”

A tsarin NPA, dukkan ribar da aka samu sai an fara zuba ta dungurugum a asusun TSA da ke CBN tukunna.

Sai dai kuma a wata wasika da NPA ta aika wa Intels a ranar 19 Ga Afrilu, ta ce tilas ko dai kamfanin ya bi ka’idojin da ta shar’anta, ko kuma a soke kwangilar dungurugum. Inda ta kara cewa ta yi wa Intels kawaici da jinkai inda ta yarda su rika yin ajiya a wasu bankuna biyu kacal baya ga TSA a CBN.

Share.

game da Author