Tsohon Shugaban Kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya bayyana cewa a yanzu wata babbar matsala da ta mamaye Ghana, ita ce tururuwar mazauna karkara zuwa cikin birane, yadda ta kai an yi watsi da karkara ana neman tarewa birane dungurugum.
Mahama ya yi wannan bayani ne a wurin wani taron da cibiyar jaddada ingantaccen shugabanci ta Olusegun Obasanjo ta shirya a ranar Talata, a dakin taro na Shehu ‘Yar’Adua da ke Abuja.
Tsohon shugaban na Ghana ya ce wannan babbar barazana ce, domin hakan na kawo cikas wajen kokarin gwamnati na maida hankali wajen kai ayyukan ci gaba a cikin karkara. Mahama ya ce ya na da muhimmanci Nijeriya ta saisaita tafarkin shugabanci domin saisaitar Najeriya tamkar saisaitar Afrika ce gaba daya.
“Kafin Ghana ta samu ‘yanci, kashi 25 na al’ummar kasar ne ke cikin birane, saura kashi 75 kuma su na cikin karkara. Amma a zaman yanzu kashi 47 na cikin birane, 43 ne ke cikin karkara. Kun ga kenan na cikin birane sun haura yawan mazauna karkara.”
Domin kara tabbatar da ci gaba a Afrika ta yamma. Mahama ya yi kira ga Nijeriya da ta daina shakkun hadewar Afrika ta Yamma a wasu fannoni na cinikayya, domin ita uwa ce mai-bada-mama.
Ya kuma yi tsokacin cewa Afrika ta yamma na da tasiri sosai a duniya. Inda har ya jaddada cewa tuni nahiyar Afrika ta Yamma ta kaddamar da juyin turun ta inda ta rabu daga mulkin sojoji ta koma dimokradiyya.
Dalili kenan ya ce bala’in guguwar sauyi irin ta Larabawa, wanda aka fi sani da ‘Arab Spring’, ba za ta taba afkuwa a Afrika ta Yamma ba, domin mu tuni mun rigaya mun karbi turbar dimokradiyya. Abin da ya rage kawai shi ne kara tabbatar da shugabanci mai inganci a kasashe.
“Duk matsala iri daya Najeriya ke fuskanta da ’yar’uwar ta Ghana.” Inji Mahama.
Tun da farko sai da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya gabatar da takarda inda ya nuna irin kokarinda yay i wajen saisaita Nijeirya da Afrika a kan sahihin shugabanci, ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa.
Shi ma shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya yaba wa Obasanjo musamman a kan farfado da jami’ar, kokarin kakkabe cin hanci da rashawa ta hanyar kafa hukumomi irin EFCC, ICPC da sauran su.
Ya kuma jinjina wa Obasanjo saboba jiriyar da ya nuna ya koma karatu, inda ya yi digiri na daya har zuwa na uku a jami’ar NOUN. Shi ya sa Abdalla ya ce Obasanjo ya nuna wa duniya cewa girman mukami ko yawan shekaru ba zai hana mutum ya nemi ilmi ba.
Ya kuma bayyana cewa ya zuwa yanzu Jami’ar NOUN ta na da dalibai sama da dubu 300.