Za a iya kiran Guguwar Buhari, guguwarjuyin juya hali. Guguwar,wacce ta tirnike kasar nan a cikin 2014, har ta yi sanadiyyar nasarar jam’iyyar APC a cikin 2015, ta yi awon gaba da mulkin jam’iyyar PDP na shekaru sha shida.
Dalilan kiran wannan guguwa da suna juyi, ya zo daidai ne da irin halayya da dabi’ar sabon salon siyasar da matasa ko na ce talakawa suka dauka a kusan fadin kasar nan, ta honyoyin sadaukarwar da suka nuna wa Muhammadu Buhari a lokacin kamfen da kuma ranakun zabe.
A lokacin da jam’iyya mai mulki a lokacin, PDP ke ta rabon kudin yakin neman zabe, kamar ruwan sama, a gefe daya kuma talakawa sun mika wuya sukutum wajen mara wa dan takarar jam’iyyar adawa, APC, Muhamadu Buhari baya tare da amsa kiran da jam’iyyar sa ta yi na a fito a tallafa masa da kudin kamfen.
A ta su gudummawar, talakawa da sauran masu karamin karfi sun amsa kira ta hanyar rika sayen katin da ake kankarewa ana tura lambobi, wanda duk katin da ka saya, to kudin zai shiga ne asusun tara wa Buhari kudin kamfen. A haka jama’a su ka rika yin kumumuwa su na cire naira dari har zuwa naira dari biyar su na sayen kati.
Kama daga manya da masu kananan saide-saide, ‘yan tireda, makada da mawaka, masu yankan farce da masu wankin takalma, ‘yan dako kai hatta almajirai ma ba a bar su a baya ba, wajen tallafa wa Buhari.
Yayin da zabe ya zo, Guguwar Buhari ta nuna ba sani ba sabo, ba babba, ba yaro. Da ta tirnike Arewa har sai da ta mamme yankin Arewa ta Tsakiya, wato jihohi irin su Benuwai. Tsananin murna ya sa a Arewa an rika yin hadayar yanka dabbobi nau’i daban daban, kama daga shanu, rakuma, tumakai da raguna, awaki, kaji da zabbi.
Wadannan rukunnan jama’a sun yi wannan sadaukarwa ne a bisa yakini, fata da kuma tunanin cewa Buhari na hawa mulki zai fara share musu hawayen su. Babbar damuwar talakan Arewa a tafiyar guguwar Buhari, ba ta wuce a kama duk wadanda suka wawuri kudin Nijeriya a daure su ba. Sai kuma batun kashe-kashen Boko Haram, da sauran matsalolin da ake ganin mulkin PDP ne ya haifar da su.
A tunanin da dama shi ne Buhari zai bi dukkan ‘yan siyasa da suka rike manyan mukamai a garkame su, bayan an kwace kudin su, tamkar yadda ya y i a mulkin sa na farko, tsakanin 1983 zuwa 1985.
Yanzu dai shekaru biyu kenan tun bayan rantsar da Buhari kan mulkin Nijeirya. Yayin da wasu ke sam-baka, akwai da yawan gaske masu guna-gunin cewa a gaskiya, ba haka suka zata ba.
A fili ta ke cewa gwamnatin Buhari ta yi rawar gani wajen dakile Boko Haram, an kwato sama da ‘yan matan Chibok dari sannan kuma ‘yan gudun hijira na ta kokarin komawa gidajen su da garuruwan su.
A fannin tattalin arziki kuwa, farkon gwamnatin Buhari ta rika kai dauki ga jihohi ta hanyar ba su tallafin kudaden tdamo su daga matsalar rashin kudi. An shigo da tsarin asusun bai daya, kwaya daya tilo, wato TSA, ta yadda aka dakile hanyoyin da ma’aikatan gwamnati ke satar kidi, ga kuma yawan wadanda ake kamawa ana gurfanarwa a koto, bayan an karbo wasu kudi da kadarorin da suka danne.
Shin duk wadannan sun isa ne? Shin a idon talakawan Arewa iyakar abin da suke ko kenan? Ko akwai wasu matsaloli ne a kwance kasa ba a kai ga sni ba?
Matsalar yaki da cin hanci da rashawa
Tashin farko, yaki da cin hanci da rashawa da Buhari ya dauko bayan yah au mulki, ya ci karo da irin wanda ya yi a zamanin mulkin sa na sojoji. A wannan karo, alamomi sun fara nunawa tun daga farko cewa shirin ya samu sartse ganin yadda APC ta hau mulki tare da kwashe-kwashen wadanda ake zargi da aikata wawurar kudade.
Kusan ADC ta hau mulki tare da tsofaffin gwamnoni sha biyar da EFCC ke kan binciken su a lokacin da INEC ta ba su damar su tsaya takarar sanata. Cikin su kuwa har da shugabn majalisar gaba dayan ta da kuma shugaban kwamitin kasafin kudi Danjuma Goje.
Yayin da gwamnatin Buhari ta cika shekara biyu, da daman a tababar nasarar shirin san a yaki da rashawa, ganin yadda manyan ‘yan siyasa da ake zargin sun wasuri kudade har yau ba a daure kowa ba.
Sannan kuma akwai zargin yadda ba a kama wadanda suka tsallake daga jam’iyyar PDP zuwa APC ana tuhumar su. Misalin irin wannan shi ne, mamakin da ake yi yadda EFCC ta sha bayyana cewa ta na cigiyar Sanata Saminu Turaki, gwamnan Jigawa 1999 zuwa 2007, wanda suka ce an sha zama kotun da ake tuhumar sa ba ya zuwa, haka kuma ba ya aika wakili.
Mamakin da ‘yan adawa ke yi, shi ne yadda Saminu ke yawo amma su jama’an ba su kama shi ba. An sha ganin sa a cikin taro, ciki kuwa har da daurin auren Zahra Buhari, ‘yar shugaban aka da a ka yi a Daura.EFCC Acting Chairman, Ibrahim Magu
Jama’a sun fara hasala
Ranar 29 Ga Mayu, 2015, jama’a sun yi wa gwamnan Neja mai barin gado a lokacin, Babangida Aliyu, korar-kare, a wurin bikin mika milki ga sabon gwamna, na APC. Ba don jami’an tsaro sun yi harbi sama domin razana dimbin mutanen da suka fara jifar tsohon gwamnan ba, to da har riga sai sun kai ga yaga masa.
Sai dai kuma abin mamaki shi ne yadda reshe ya juye da mujiya, tun kafin ma a shekara biyu a kan mulki. Sanatoci da ‘yan majalisar tarayya na APC da dama an jejjefe su a mazabun su. Alamomi da dama sun nuna cewa da yawan su ba za su iya komawa kan kujerun su a karo na biyu ba. Kenan hakan na nufin ba za a yi “Sak” a zaben 2019 ba.
Rashin kyakkyawar mu’amala tsakanin jami’an tsaro da farar hula.
Wata matsala da ake kallo a wannan gwamnati shi ne yadda jami’an sojoji da ‘yan sanda ke gallaza wa farar hula. Wannan matsala ta yi muni sosai, yadda babu wani abu tsakanin jami’an tsaro da farar huta sai duka, gwale-gwale da sauran nau’o’i na zallaza wa, sannan abin ya zama ruwan dare. Da yawan mutane na korafin cewa a wannan bangare ba su ma ga wani bambanci da gwamnatin da ta shude ba, wato babu wani canji.
Dusashewar haske a Kaduna, Benuwai da Taraba
An yi tunanin a cikin shekarar farko Buhari zai kawo karshen kashe-kashe da ke faruwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankin kudancin Kaduna, Benuwai da Taraba da sauran wurare. Yawaitar wadannan tashe-tashen hankula musamman a kudancin Kaduna da Benuwai, sun rage karsashin APC da har shi kan sa shugaban kasa.
Munin wadannan rigingimu ne ya sa har jihar Benuwai, wacce APC ke mulki ta yi shelar kafa dokar haramta kiwon dabbobi a jihar ta. Wannan kuwa ba karamin cikas ba ne ga APC a jihar Benuwai.
Gunagunin da ake yi a Kano da Jigawa da Katsina
Premium Times Hausa ta binciko cewa Kanawa na jin haushin yadda suka tula wa Buhari kuri’u har kusan milyan biyu, amma har yau ga shi an shekara biyu, bai kai ziyara ko ta awa daya a Kano ba. Abin lura shi ne irin yadda aka yi wa Buhari ruwan kuri’u, wadanda yawan masu zaben duk suka zabi APC.
Buhari ya samu kuri’u milyan 1.9 da ‘yan kai, yayin da Jonathan ya samu dubu 225 kacal.
Premium Times ta binciko yadda a Kano aka jin haushin duk da cewa Buhari bai taba zuwa ko sau daya tun bayan hawan sa mulki ba, haka kuma babu wani aiki na gwamnatin tarayyya da ake kaddamar a cikin wadannan shekaru biyu.
Mamaki da ta’ajibi ya kara kama jama’a da dama ganin yadda aka yi munanan gobara har guda biyu a Sabongari da Kantin Kwari, kuma aka kiyasta ta ci dukiya ta bilyoyin nairori a kasuwannin biyu, amma bai je ko jaje ba.
Sai dai kuma a cikin kasafin kudi na 2017, da farko an ware makudan kudade da za a gina birnin shirya fina-finai, wato Film Village a Kano.
Premium Times ta gano cewa yawancin mutane sun ki goyon bayan shirin kafa birnin ne saboda a cewar su, su na fama da tulin matsaloli wadanda ke da bukatar daukin gaggawa daga gwamnatin tarayya, amma sai aka rasa abin da za a yi masu sai Film Village.
A zantawar da ya yi da Premium Times Hausa, wani direba mai suna Dahiru, ya bayyana a cikin fushi cewa, “Ni fa wallafi na zabi Buhari ne ba don ya zo ya inganta harkar fina-finan Hausa ba. Ina ruwan mu da finafinan Hausa, alhaili ga tulin matsalolin da ke damun mu.”
Kai ni fa da na san za a shekara biyu ba a yi mana komai ba, wallahi da ban tsaya bata lokaci na yi wa APC wahala ba. Shin wai ba su san yadda titin Zariya zuwa Kano ya lalace ba ne? ko don ba ya kashe ‘yan uwan su sai talakawa ya ke kashewa, shi ya sa ba su damu ba?” Inji Dahiru, diraban da ke jigila daga Kano zuwa Abuja.
A bisa dukkan alamu dai za a iya cewa rashin lafiyar da Buhari ke fama da ita ce ta sa masu gunaguni ba su fara nuna fushin su a sarari ba.
Bincike a Jigawa a nuna yadda ake gunagunin cewa yawancin mukamai na gwamnatin tarayya, duk a Kazaure aka bada su. Daga Kazaure minista ya fito, haka kuma Darakta Janar na NYSC shi ma dan Kazaure nene, garin da ke da kusanci da Daura, kuma ana yi masa kallon garin da Buhari ke takama da shi, baya ga Daura.
Zaben cike gurbin dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Mashi da Dutsi a jihar Katsina, ya nuna yadda hasken APC ya fara dusashe wa a jihar da shugaban kasa ya fito. APC dai ta samu kuri’u 27,968 yayin da PDP ta samu 19,451, a wadannan kananan hukumomi biyu da ke shiyyar sanata daya da shugaban kasa, kuma su na kusa da Daura.
Dama kuma bayan kammala zaben shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Salisu Majigiri, ya bayyana cewa ba su amince da zabenn ba, sannan kuma za su daukaka kara, domin a zargin da ya yi, ya ce APC ta saci akwatan zabe makare da kuri’u, kuma an yi amfani da karfin mulki da karfin jami’an tsaro.
Premium Times dai ta gano cewa akasarin manyan ma’aikatan jihar Katsina, tun daga kwamishinoni, ‘yan majalisa na tarayya, na jihohi da sauran kusoshin gwamnati sai da suka je wurin zaben a Mashi da Dutsi.
Duk da cewa akwai wadannan matsaloli, akwai da yawa a Arewa da ke ganin cewa an yi abin kwarai, kuma gara yau da jiya, wato gwamnatin baya ta Jonathan, wacce wasu ke ganin cewa ita ce silar jefa kasar nan cikin jangwangwama.