HAJIN BANA: Mahajjata za su biya naira 38,000 kudin hadaya

0

Hukumar kula da aikin haji ta kasa ta umurci dukkan hukumomin dake kula da ayyukan haji a jihohi da su karbi naira 38,000 a hannun maniyyata hajjin bana kudin hadaya.

Hukumar tace za a ajiye wadannan kudade ne a bankin Jaiz.

Hukumar tace tayi haka ne saboda gujewa rudanin da akan samu inda wasu ke ganin ba a yi musa hadaya bayan sun biya.
NAHCO tace yin hakan zai warware irin wadannan matsaloli da zarge-zarge.

Share.

game da Author