Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa tsohon gwamnan da ya karbi mulki a hannun sa, Ibrahim Shehu Shema ya yi amfani da asusun ajiya a bankuna daban-daban, har sama da asusu 100.
Masari ya yi wannan bayani ne ranar Lahadi da ta gabata yayin yda ya ke jawabi wurin taron Katsinawa mazauna Abuja, a dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.
Masari ya ce gwamnatin sa ta gaji rashin kudi, rigingimu da harkallar kudade daga gwamnatin da ta gabata, wadda ya gada.
Ya buga misali da wayan ma’aikatan bogi, aringizon albashi da sauran su. Don haka ne ma ya nuna damuwar sa in da ya ce sai iska ya tarad da kaba na rawa, wato matsalar tattalin arziki ta zo ta kara shafar jihar.
‘’Naira milyan 7.9 kacal muka gada a cikin asusun biyan albashi na jihar.
Haka sauran asusun ajihar dukkan su babu komai sai abin da ba a rasa ba. To kuma yanzu babbar matsalar mu shi ne yadda mafi yawan kananan hukumomin Katsina kudin da suke samu daga kason gwamnatin tarayya, ba ya ma isar su biyan albashi.
‘’Mu kanmu a matakin jiha sau da dama kudaden tallafin da gwamnatin tarayya ke rabawa, kamar kudin ceto jihohi da ga durkushewa mu ke timkaho. Ga shi kuma matsaloli sun yi mana katutu ga kuma talauci da aka ce Jihar Katsina ce ta uku a kasar nan.”
Masari ya yi kira ga manyan masu ruwa da tsakin jahar da su taimaka wajen zuba jari a Katsina domin matasa su samu aikin yi, sannan kuma a dawo da martabar da aka san jhar Katsina na da ita. Gwamnan ya kuma jajanta irin yadda ya samu yawaitar lalatattun gine ginen-gwmanti, musamman makarantun firamare, sakandare, manya da kananan asibitoci, wadanda ya ce amma duk gwamnatin sa ta gyara su.
“Abin takaici ne halin da jihar Katsina ke ciki na matsin rayuwa da koma-bayan tallain arziki. Bai kamata a ce mu na a matsayin da mu ke a yanzu ba. Ina kira kowa ya mike tsaye mu sake farfado da jihar Katsina.
Kwamishinoni bakwai da shugabannnin wasu bangarorin hukumomi biyu ne suka yi wa dimbin jama’ar da suka taro jawabin nasarorin da suka samu a cikin shekara biyu.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Mustapha Inuwa, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin dakile matsalar tsaro, ya bayyana yadda masu rike da sarautun gargajiya, ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa ke da hannu wajen matsalar satar shanu a jihar.
Inuwa ya ce sai barawo ya saci maayan shanu wadanda farashin kowan a kasuwa zai kai naira dubu 150, amma sai a sayar musu a kan naira dubu 30 kacal.