Gwamnatin jihar Kaduna zata hada hannu da kamfanin Notore domin bunkasa fannin noma a jihar

0

Babbar kamfanin sarrafa takin gona mai suna Notore Chemical Industries Plc zata hada kawance da gwamnatin jihar Kaduna domin saka jari domin bunkasa fanin aiyukkan gona a jihar.

Shugaban kanfanin Onajite Okoloko da tawagarsa sun ziyarci gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai inda suka sanar da niyyarsu na saka jari a jihar domin bunkasa fannnin aiyukan gona a jihar.

Okoloko ya ce bayan sarrafawa da siyar da takin zamani da kamfaninsu ke yi, za ta ci gaba da taimaka wa manoma don samun yalwan abinci a jihar.

Burinmu shine abinci ya yalwata a kasa Najeriya kuma sanin kowa ne cewa jihar Kaduna zata iya zama kan gaba don samun nasarar haka ganin cewa jihar tafi kowace jiha noman masara da waken soya a kasar nan.”

Ya kuma sanar da cewa suna koyar da manoma kan dabarun aiyukkan noma na zamani a filayen.

“Sakamakon dabarun aiyukkan noman zamanin da muka koya wa manoma yasa an samu amfani mai yawa na albasa daga jihar Kebbi da kuma Kabeji da aka samu a jihar Filato.”

Da yake tofa albarkancin bakin sa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I ya ce gwamnati zata ba kamfanin duk gudunmawa da goyon bayar da take bukata domin samun nasara akan hakan.

Share.

game da Author