Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ce jihar ta kusa kammala shirin da ta keyi na kafa wata doka da zai hana kiwata dabobi a ko ina a fadin jihar.
Gwamnatin tace yin hakan zai rage rikici dake aukuwa tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
Ortom ya fadi hakan ne a Abuja da yake ganawa da mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbanjo kan yanayin tsaro a jihar Benue.
Yace dokar zata samarda zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya, kuma gwamnatin na neman hadin kan Manoma da makiyaya akan hakan.
“ Za mu kafa wannan dokar ne domin samar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyar da suke kiwo da noma a dazukan jihar.