Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yace gwamnatin jihar ta dakatar da shawarar da ta dauka na rufe sansanonin ‘yan gudun hijira saboda burbudin aiyukkan Boko Haram da har yanzu jihar ke dan fama da su.
Ya fadi hakan ne a bukin mika wa jihar gudunmuwar wasu gine-gine da gidauniyar ‘Victims Support Fund VSF’ ta yi a garin Bama ranar Talata.
Gwamnan ya ce gwamnati ta amince da shawarar dakatar rufe sansanonin ne kamar yadda ada ta shirya saboda kira da shawarwarin da jami’an tsaro suka bata da ta dada jinkirtawa tukuna.
“Idan mutane suka koma garuruwansu ya kamata ace rayuwarsu ta koma kamar yadda take da ne wanda tabbaci da samun haka ya rataya a kan mu ne”.
Kashim Shettima ya kara da cewa duk da haka za su ci gaba da aikin gina wuraren da suka lalace sanadiyyar hare-haren Boko Haram. Ya kuma godewa gidauniyar kan gudunmuwar da take ba jihar.
Ya ce a shekarar 2015 gidauniyar ta ba jihar gudumawar kayayyakin gini da ya kai Naira miliyan 250 domin gina wuraren da za su amfani mutanen jihar.
Daga karshe mataimakin gidauniyar VSF Tijjani Tumsa ya ce gidauniyar za ta ci gaba da tallafa wa jihar da irin wadannan taimako.