Idan dai kana raye bazaka gaji da ganin abubuwan al’ajabi ba. Wannan karon a garin Jos Babban birnin jihar Filato wani abin tsoro, dariya da tashin hankali ya faru da wadansu ‘yan uwa biyu inda Allah yayi ma daya rasuwa daya kuma yana raya.
Shi wanda ya riga mu gidan gaskiya Choji Zeng dan shekara 35 ne ya tsorata al’ummar da ke shirin yi masa sutura a inda dai-dai dan’uwansa Gyan ya matso kusa dashi sai ya rike masa hannu gam, akayi-akayi dashi ya saki hannun nan yaki sai da jami’an dake kula da dakin ajiye gawa na asibitin suka kawo masa dauki.
Gyang yana ta rokon gawan dan-uwan nasa da ya sake shi ya na cewa “Choji saboda menene ka rike ni ko kana so mutafi tare ne.’’
Da kyar dai Allah yayi aka samu aka bambare hannun Choji daga jikin dan-uwansa.
Ma’aikatan dakin ajiye gawa na asibitin sun ce hakan ba shi bane karo na farko da irin hakan ke faruwa a dakin.